Sarkin Ife ya bai wa jikan Shagari mukami

Sarkin Ife ya bai wa jikan Shagari mukami

- Mai martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II ya nada Bello Bala Shagari a matsayin manajan daraktan kungiyar RAYLF-AFRICARAYLF-AFRICA

- Bello Bala Shagari ya kasance jika ga Shehu Usman Aliyu Shagari, shugaban kasa na farko da aka zaba a Najeriya wanda soji suka mika wa mulki a 1979

- Nadin nasa zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumba 2020 kuma za a sake waiwayarsa bayan shekaru biyu

Sarkin Ife, mai martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II ya nada Bello Bala Shagari a matsayin manajan daraktan kungiyar 'Royal African Young Leadership Forum' (RAYLF-AFRICA).

Nadin na kunshe ne a wata takardar da ya aika wa Bello Bala Shagari, wacce Dr. Ayobami O. oyedare yasa hannu.

Bala wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar matasan Najeriya ya kuma kasance jika ne ga Shehu Usman Aliyu Shagari, shugaban kasa na farko da aka zaba a Najeriya wanda soji suka mika wa mulki a 1979.

Sarkin Ife ya bai wa jikan Shagari mukami
Sarkin Ife ya bai wa jikan Shagari mukami Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kamar yadda wasikar ta bayyana, "Mai martaba yana sha'awar salonka, hazaka da kuma yadda kake bada goyon baya ga gyaran mulki a Afrika ta hanyar ilimi tare da bai wa matasa karfin guiwa.

"Bayan duban haka, mun fahimci cewa akwai tunanin makamancin tsakaninmu kuma muna bukatar a sanya ka duba shugabancin RAYLF.

"Na rubuto wasikar nan ne don tabbatar da nadinka a matsayin daraktan RAYLF."

KU KARANTA KUMA: Tsaro: Umahi ya soki sauya shugabannin tsaro, ya bai wa Buhari shawara

Wannan mukamin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumba 2020 kuma za a sake waiwayarsa bayan shekaru biyu.

A wani labari na daban, mun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da takwaransa na Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu, mai martaba Muhammad Iliyasu Bashar.

Sarakunan biyu 'yan uwan juna sun kai ziyarar ne a yau, Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2020, kamar yadda wata sanarwa daga majiyar fadar ta wallafa a shafin sada zumunta.

Alhaji Muhamad Bashar, tsohon soja a rundunar soji ta Najeriya, ya zama sarkin Gwamdu a shekarar 2005 bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tsige tsohon sarki, Mustapha Jokolo Haruna.

Mai martaba Bashar ne sarkin Gwamndu na 20 tun bayan kafuwar masarautar a karni na 18.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel