An kashe sabbin mutane 33 a kudancin Kaduna

An kashe sabbin mutane 33 a kudancin Kaduna

Mutane 33, yawanci yara mata da yara sun rasa rayukansu yayinda yan bindiga dadi suka sake kai hari kauyukan masarautar Atyap dake karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Amma hukumar yan sanda ta ce mutane 21 aka kashe.

Daily Trust ta tattaro cewa hare-haren sun auku ne lokaci guda tsakanin karfe 11 na daren Laraba da karfe 1 na dare a kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori da Kurmin Masara a masarautar Atyap.

Wata majiya ta bayyana cewa saboda ruwan saman da akeyi, yan bindigan sun ci karansu ba babbaka duk da dokar ta bacin da gwamnatin ta sa.

Wani mazaunin kauyen Atak'mawai (Kurmin Masara), Irimiya Gandu, wanda ya tabbatar da harin ya ce rayuka akalla 12 sun salwanta yayinda aka kona gidaje da yawa.

Ya ce maharan sun dira unguwar misalin karfe 1 na dare yayinda al'umman kauyukan ke bacci.

"Lokacin da na fara jin karan harbin bindiga na shiga gida na kwashi iyalaina muke boye wani waje. An kashe mutane 12, yawanci yara da mata." Yace

KU KARANTA: Ba wani sabon abu ne, mun sani - Hukumar Sojin Najeriya ta mayarwa Amurka martani kan shigan yan ta'adda Arewa maso yamma

Wani mazaunin Apiojyim dake garin Kibori, Jonathan Ishaya, ya ce mutane bakwai aka kashe a daren yayinda aka kai musu hari.

A cewarsa, yan bindigan sun dira kauyen ne misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

"Niyyarsu shine su kawo harin bazata, amma yayinda suka iso, sai suka isar da matasanmu na sintiri kuma sukayi musayar wuta." Yace

"Mun birne mutane bakwai yau (Alhamis), har da dan shekara 80." Ya kara.

An kashe sabbin mutane 33 a kudancin Kaduna
An kashe sabbin mutane 33 a kudancin Kaduna
Asali: Twitter

Wani takardan da Kakakin kungiyar al'ummar kudancin Kadna SOKAPU, Luka Biniyat, ya saki ya ce jama'an masarautar Atyap 33 aka kashe cikin kauyuka biyar: Apiojyim, Kibori, Apiako, Atakmawe da Magamiya.

Ya mika kokon baran kungiyar ga kasashen duniya a kawo musu dauki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel