Hotuna: Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya tafi Senegal don hallartar jana'izar ɗan Sheikh Inyass
- Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II ya shilla birnin Kaolack da ke Senegal a yau Alhamis
- Muhammadu Sanusi II ya tafi kasar ne domin hallartar jana'izar Sheikh Tijjanni Nyass
- Marigayin ya rasu ne a ranar Litinin yana da shekaru 65 a duniya
Tubabben tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis ya bar Najeriya Najeriya don zuwa Kaolack, Senegal inda zai hallarci jana'izar Sheikh Tijjani Nyass dan Sheikh Ibrahim Nyass.
Marigayin Malamin ya rasu ne a ranar Litinin yana da shekaru 65.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: COVID-19: Buhari ya sabunta dokar kulle da makonni hudu

Asali: Twitter
A sakon ta'aziyarsa ga Shugaba Macky Sall, gwamnati da al'ummar Senegal da dimbin mabiya darika Tijaniyya a Najeriya, Shugaba Buhari ya nuna bakin cikinsa game da rasuwar malamin.
Buhari ya ce, "Mun yi bakin samun labarin rasuwar Khalifa, Sheikh Ahmed Nyass da ya rasu a Senegal.
"Sheikh Ahmed Nyass da ya gaji mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Nyass bai bawa mabiya mahaifinsa kunya ba.
"Za a rika tuna wa da shi saboda dimbin hidiman da ya yi wa addinin islama da mabiya darikarsa har da wadanda ke Najeriya."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng