'Yan sanda sun kama kwantaina mai kafa 40 cike da tramol da kodin

'Yan sanda sun kama kwantaina mai kafa 40 cike da tramol da kodin

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas sun kama wata babbar motar dakon kaya (kwantaina mai tsawon kwafa 40) a cike da wasu miyagun kwayoyi da ake zargin tramol ne da kodin.

An kama kwantainar ne tun ta na kan ruwa a tashar jiragen ruwa da ke yankin Apapa.

Jami'an tawagar hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi da na hukumar fasa kwauri ta kasa (NCS) sun isa wurin kwantainar bayan jami'an 'ya sanda sun tsareta.

Ko a 'yan kwanakin baya bayan nan sai da kwamand 'B' ya kama irin wadannan miyagun kwayoyi tare da mika wadanda ake zargi da safararsu zuwa hannun hukuma domin a gurfanar dasu.

Ana tsammanin cewa rundunar 'yan sanda za ta mika kwantainar zuwa hannun hukumomin da su ka dace domin zurfafa bincike.

'Yan sanda sun kama kwantaina mai kafa 40 cike da tramol da kodin
'Yan sanda sun kama kwantaina mai kafa 40 cike da tramol da kodin
Asali: Twitter

A ranar Talata ne mai bawa sugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana cewar safarar miyagun kwayoyi na daga cikin abubuwan da ke kara rura wutar rashin tsaro a cikin kasa.

DUBA WANNAN: Sarkin Kano da Sarkin Bichi sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu

A cewars Monguno, batun safara da sarrafa miyagun kwayoyi a Najeriya na daga cikin batutuwan da majalisar zartarwa ta kasa (NEC) ta tattauna a zamanta na karshe.

A cewarsa, Najeriya ta tashi daga bolar jibge miyagun kwayoyi zuwa cibiyar sarrafa miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa a kwanakin baya hukuma ta rufe wasu manyan dakunan sarrafa miyagun kwayoyi guda 17 a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel