Fusatattun matasa sun farke rufin majalisar Edo, sun sace sandar iko

Fusatattun matasa sun farke rufin majalisar Edo, sun sace sandar iko

Wasu fusatattun matasa sun farke rufin ginin majlisar dokokin jihar Edo tare da sace sandar ikon zaman majalisar.

Da safiyar yau, Alhamis, ne 'yan sanda suka mamaye farfajiyar majalisar jihar Edo, sa'o'i kadan bayan tsige mataimakin kakakin majalisar, Yekini Idiaye, wanda 'yan majalisar jihar suka yi yayin zaman majalisar a Benin.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta 1 da wasu 'yan majalisa hudu, a ranar Litinin, sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wadanda suka bi ayarin Idiaye sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas, Dumez Ugiagbe mai wakiltar mazabar Ovia ta arewa maso gabas.

Duk sun bayanna goyon bayansu ga Fasto Ize-Iyamu a gidan sa da ke Benin. Amma kuma Roland Asoro, mai wakiltar mazabar Orhionmwon II an nada shi a matsayin mataimakin kakakin.

DUBA WANNAN: Hari kan tawagar gwamna: Hedikwatar tsaro ta mayar wa da Zulum martani

Sai dai, a yayin da majalisar ke zamanta wasu gungun matasa sun dira majalisar domin nuna goyon bayansu da biyayya ga gwamna Godwin Obaseki, wanda ke takarar neman tazarce a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Ana zargin cewa za a yi amfani da mambobin majalisar dokokin jihar Edo da jam'iyyar APC keda rinjaye domin tsige gwamna Obaseki gabanin zaben da INEC za ta gudanar a cikin watan Satumba.

Wannan ba shine karo na farko da matasa su ka fara cire rufin majalisar jihar dokokin jihar Edo ba, hakan ta taba faruwa a shekarar 2014 bayan barkewar rikici a tsakanin mambobin APC da PDP a majalisar

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng