Karin 'yan Najeriya 457 sun kamu da korona, jimilla 44,890
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 457 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:37 na daren ranar Laraba 5 ga Augustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 457 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-137
FCT-76
Plateau-40
Rivers-35
Enugu-34
Oyo-25
Abia-23
Delta-12
Edo-11
Ebonyi-11
Cross River-10
Kwara-10
DUBA WANNAN: Yaki da COVID-19: Ganduje ya zama gwarzo a tsakanin gwamonin Najeriya
Kaduna-9
Anambra-7
Ogun-5
Imo-3
Bauchi-3
Osun-2
Nasarawa-2
Kano-1
Ekiti-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Laraba 5 ga watan Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 44,890 .
An sallami mutum 32,165 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 927.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng