Babu yadda kuka iya, wajibi ne ku amince da tubabbun yan Boko Haram - Buhari ya al'ummar Arewa

Babu yadda kuka iya, wajibi ne ku amince da tubabbun yan Boko Haram - Buhari ya al'ummar Arewa

An umurci shugabannin gargajiyan garuruwan da rikicin Boko Haram ya addaba su hada kai da hukumomi wajen hana mutane nuna kiyayya ga tubabbun yan ta'addan Boko Haram,.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki ranar Laraba da TheCable ta gani.

An yaye tubabbun yan Boko Haram da aka horar kuma aka sauyawa tunani 600 a watan Yuli, amma mutan jihar Borno sun bayyana cewa basu yadda a dawo da su cikin al'umma ba.

Amma, kakakin Buhari ya ce shirin bai hada da rikakkun yan ta'adda ba kuma ya zama wajibi sarakunan gargajiya su san nayi domin amincewa da tsaffin yan ta'addan ko kuma su koma gidan jiya.

"Wannan shirin ba na rikakkun yan ta'adda bane. Kawai ana daukan tubabbun da aka tursasawa daukan makamai ne, kuma akwai wadanda aka shigar Boko Haram karfi da yaji." Shehu Yace

"Yayinda ake yayesu, ana da tabbacin cewa tsoffin yan ta'addan sun tuba kuma sun zama yan kasa na gari. Basu da sauran wani illa ga al'umma."

"Idan aka tabbatar da hakan game da su, al'umma na hakkin karbansu. Ama idan shugabannin al'umma basu son su koma ta'addancin da suka tuba, wajibi ne su hada kai da hukumomi wajen hana nuna musu kiyayya."

KU KARANTA: Yan ta'addan Al-Qa'ida sun fara shiga jihohin Arewa maso yamma - Amurka ta ankarar da Buhari

Babu yadda kuka iya, wajibi ne ku amince da tubabbun yan Boko Haram - Buhari ya al'ummar Arewa
Babu yadda kuka iya, wajibi ne ku amince da tubabbun yan Boko Haram - Buhari ya al'ummar Arewa
Asali: UGC

A bangare guda, fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta karyata jita jitar da ake yada wa na cewa an dauki wasu daga cikin tubabbun yan Boko Haram aiki a Rundunar Sojojin Najeriya.

Wannan jita jitar ya bazu sosai a dandalin sada zumunta hara ta kai ga wasu 'yan Najeriya da dama sun fara shakku a kan shirin gwamnatin tarayya na sauya halin tubabbun yan taadan.

Jita jitar ta kara karfi jim kadan bayan Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ce sojoji ne suka kai wa tawagarsa hari ba yan Boko Haram ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel