CACOVID ta bawa Kano tallafin kaya na Naira miliyan 500

CACOVID ta bawa Kano tallafin kaya na Naira miliyan 500

Hadakan kungiyoyi masu fafutikar kawar da COVID-19 (CACOVID) ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin kayan abinci na kimanin Naira miliyan 500.

Kayayyakin da ta bawa jihar sun hada katon din indomie 224,100, katon din taliyya 84,116, katon din makaroni da buhunan flawa 112,055.

Saura sun hada da buhunnan sukari 112,382 a kananan buhu na kilogram 5, buhunannan shinkafa 112,055 na kilogram 10 da buhunnan gishiri 112,060.

CACOVID ta bawa Kano tallafin Naira miliyan 500
CACOVID ta bawa Kano tallafin Naira miliyan 500. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Da ya ke mika kayan tallafin a karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano a ranar Talata, wakiliin kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Abdulkadir Sidi ya ce sun bayar da tallafin ne domin tallafawa gwamnatin wurin yaki da korona.

DUBA WANNAN: Ni ne nayi sanadin waƙar Jarumar Mata - Sunusi Oscar

Ya kuma jadadda cewa kungiyar tana da niyyar tallafawa gajiyayyu miliyan 1.67 da kayan abinci a jihohi daban daban na Najeriya.

"Muna ware gajiyayyu miliyan 1.67 da za mu tallafawa a Najeriya, a Kano mutane 112,055 ne za su amfana da tallafin," in ji Sidi.

A jawabinsa, gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, da ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna ya yabawa kungiyar da ya ce a baya ta bawa jihar tallafin cibiyoyin gwaji da killace masu jinya.

Ya ce wannan ya yi dai dai da tsarin gwamnatin jihar na yaki da korona wato kiyayye wa, yin magani da bayar da tallafi.

A wani rahoton, kungiyar kwararru na Afirka mai suna African Professionals Renaissance Network, (APREN), da ke Dakar, Senegal ta zabi gwamnan Kano, Umar Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi kwazo wurin yaki da COVID-19 a Najeriya.

A cikin wasikar da sakataren kungiyar Diouf Bakri Koalack, ya aike wa gwamnan, ya jinjina masa bisa jajircewarsa wurin yaki da annobar da ya karade duniya kamar yadda TVC ta ruwaito.

Kungiyar ta jadada cewa jajircewa gwamnan ya fito fili har ta kai ga Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta yaba da kokarin gwamnan domin kowa ya sani.

Bayan nazarin yadda yaki da korona ke tafiya a jihohin kasar, "...mun fahimci cewa jihar Kano ta fita zakka a wurin yaki da annobar. Hakan kuma ya faru ne saboda jajircewa da kwazon gwaman wurin yaki da annobar."

"Tun kafin bullar cutar a jihar Kano, mun gano cewa jihar ta kasance cikin shirin ko ta kwana. Bayan samun mutum na farko mai cutar a jihar, Gwamna Abdullahi Ganduje bai yi kasa a gwiwa ba wurin daukan matakan da suka dace."

"Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ta yi gaggarumin aiki wurin dakile annobar COVID 19," a cewar kungiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel