Mutane 10,946 da ke jinyar COVID-19 a gida a Legas sun samu lafiya – NCDC
- Mutum fiye da 10, 000 aka samu labarin sun warke daga COVID-19 a makon nan
- NCDC ta ce mutane kimanin 10, 900 da su ke jinyar gida a Legas sun samu lafiya
- Legas ce Jihar da ta fi kowace a Najeriya fama da yawan masu dauke da COVID-19
Jama’an Najeriya sun wayi gari a ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, da labarin cewa adadin masu jinyar cutar COVID-19 da aka sallama ya karu sosai.
A ranar Litinin, alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar da cewa mutum 20, 663 aka sallama a Najeriya. Bayan kwana guda adadin su ya zabura ya kai har 31, 851.
Abin da hakan ya ke nufi shi ne mutum 11, 188 su ka warke daga cutar a wannan gajeren lokaci.
Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar miyagun cututtuka a kasar ta yi karin bayani game da wannan lamari, ta ce ta hada ne da wadanda su ka warke a gidajensu.
NCDC ta ce alkaluman da ta tattaro a farkon makon nan ya hada da mutane 10, 946 da kafin yanzu su ka yi jinya a gida, wanda yanzu duk an tabbatar sun samu lafiya.
KU KARANTA: Sababbin alkaluman cutar COVID-19 a Najeriya
Kamar yadda hukumar ta bayyana, akwai rukunin masu Coronavirus da ake kula da su a gida, kuma sai a makon nan ne NCDC ta bukaci a ba ta rahoton wadannan mutane.
Da aka karbi rahoton masu jinyar gida, sai alkaluman wadanda aka sallama ya tashi a jiya, har ta kai jama’a su na ta aika tambayoyi domin jin abin da ya faru.
Shugaban NCDC ya ce: “Kwanan nan mu ka aikawa jihohi su ba mu rahoton wadanda su ka warke a gida. Wadannan mutane ne wanda su ka samu sauki, amma ba a dakin kula da masu COVID-19 da ke Legas su ka yi jinya ba.”
Ana sa ran yawan marasa lafiyan da su ka samu sauki zai karu da zarar sauran jihohi sun aikowa hukumar da na su rahoton kamar yadda shugaban NCDC ya bayyana a Twitter.
Kawo yanzu mutane 44, 000 su ka kamu da cutar a kasar, fiye da 30, 000 sun warke, wasu 900 sun mutu, daga ciki har da mutane 14 da su ka rasu a makon nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng