Gwamnatin Zamfara ta umurci makarantu su fara aiki a ranar 9 ga watan Agusta

Gwamnatin Zamfara ta umurci makarantu su fara aiki a ranar 9 ga watan Agusta

Gwamnatin Zamfara ta umurci a buɗe dukkan makarantun sakandare a jihar ranar 9 ga watan Augusta domin bawa ɗalibai daman rubuta jarabawar fita wato SSCE.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan yayin da ta ke dangana da manema labarai a ranar Talata kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Abdullahi ya ce jihar ta bi umurnin gwamnatin tarayya ne na buɗe makarantun domin daliban JSS3 da SS3 su rubuta jarabawar fita.

Gwamnatin Zamfara ta umurci makarantu su fara aiki a ranar 9 ga watan Agusta
Gwamnatin Zamfara ta umurci makarantu su fara aiki a ranar 9 ga watan Agusta. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ni ne nayi sanadin waƙar Jarumar Mata - Sunusi Oscar

"Saboda haka, Gwamna Bello Matawalle ya umurci ma'aikatar ilimi ta fara shirin buɗe makarantun domin yaye daliban ajujuwan ƙarshe kamar yadda gwamnatin tarayya ta umurta.

"Kamar yadda ku ke gani, mun kammala tattaunawa kuma mun duba dukkan kalubalen da za mu iya fuskanta kuma mun warware su.

"Za a buɗe dukkan makarantun kwana a ranar 9 ga watan Augusta yayin da makarantun jeka-ka-dawo za su buɗe a ranar 10 ga watan Augusta.

"Mun dauki wannan matakin ne domin bawa makarantun gwamnati da masu zaman kansu daman yin shirin jarabawar bisa tsarin kiyaye yaɗuwar Covid 19," a cewar kwamishinan.

Mr Abdullahi ya ce gwannatin jihar za ta yi wa dukkan makarantu da cibiyoyin jarabawa 193 da ke jihar feshi.

"Muna kira ga iyayen yara su tabbatar ƴaƴansu sun koma makaranta a kan lokaci kuma su bawa ƴaƴansu kayan tallafi da zai basu damar bin dokokin kiyaye ƴaduwar covid 19.

"Gwamnatin jiha za ta samar da hand sanitiza, sabulun wanki, na'urar auna yanayin zafi ko sanyin jiki da wasu abubuwa a cibiyoyin jarabawar.

"Za mu samar da ma'aikatan lafiya a dukkan makarantun da cibiyoyin jarabawar," in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na shirin buɗe sauran ajujuwan nan gaba.

Ya ce gwamnatin na duba yiwuwar buɗe sauran ajujuwan da suka hada da frimare, Jss1, Jss2, Ss1 da Ss2 a ranar 24 ga watan Augusta.

Ya yi kira ga dukkan makarantu a jihar su kiyaye dukkan dokokin kiyaye ƴaduwar COVID 19 kuma su bawa gwamnati haɗin kai don saman nasarar jarabawar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel