Dalilai 4 da yasa Shoprite za ta janye daga Najeriya

Dalilai 4 da yasa Shoprite za ta janye daga Najeriya

A ranar Litinin ne babban kantin sayar da kayayyaki na Shoprite ya sanar da cewa ya fara duba yiwuwar dena gudanar da harkokin kasuwancinsa a Najeriya.

Shoprite Holdings Limited da ke da hedkwata a kasar Afirka ta Kudu ya fitar da wannan sanarwar ne a rahoton kasuwancinsa a ranar 28 ga watan Yunin 2020.

Kamfanin ya sanar da samun ribar kashi 6.4 cikin dari na dukkan kasuwancinsa a sassar da ya ke da su a kasashe da dama duk da annobar korona amma ya ce ya dauki matakin dena harkoki a Najeriya saboda, "an samu wasu masu shaawar saka hannun jari kana da yiwu tsarin kamfanin garambawul."

Ko mene yasa kamfanin zai janye daga Najeriya?

Duk da cewa rahoton kasuwanci na kamfanin ya ana samun karuwar sayar da hajja da riba, riba na zuwa ne daga kantinan da ke Afirka ta Kudu galibi.

Kamfanin ya ce hakan ya faru ne saboda dokokin kulle da aka saka a mafi yawancin kasashen Afirka sakamakon bullar annobar korona.

Shoprite na da sassa kimanin 25 a Najeriya kuma tana da ma'aikata fiye da 2,000 kuma da dama cikinsu yan Najeriya ne.

Baya ga wannan dalilin da kamfanin ta bayar, Premium Times ta yi nazarin batun inda ta gano cewa akwai yiwuwar sauka da hauhawar Naira na daga cikin dalilan da yasa kamfanin ta dauki wannan matakin.

Dalilai 5 da yasa Shoprite za ta bar Najeriya
Dalilai 5 da yasa Shoprite za ta bar Najeriya
Asali: UGC

1. Annobar korona

Rahoton da kantin ya fitar a ranar Litinin ya nuna cewa yana hasashen cewa dokar kulle da aka saka a kasar saboda COVID 19 ya taka rawa wurin raguwar samun ciniki.

Kamfanin ya kuma ce ya kashe kimanin R327.2 miliyan a bangaren lafiya da tsaro domin tabbatar da cewa ya kiyayye maaikatarsa da kwastomomi yayin annobar.

Bugu da kari, cinikin da kamfanin ke samu ya ragu saboda babu kudade a hannun mutane sakamakon annobar da ta hana aiki da wasu hada hadan kasuwanci.

2. Rage darajar Naira da sauka da hauharwar ta

Yan kasuwa da masu saka hannun jari sun dade suna fama da kallubalen sauka da hauhawar darajar kudi da kuma yunkurin rage darajar kudi.

A watan Yuni, babban bankin Najeriya, CBN, ta mayar da darajar Naira zuwa dalla ya koma N381 a yunkurin ta na kawo daidaito.

Duk da cewa bankin ba ta sanar da haka a hukumance ba, bayanai daga FMDQ OTC ya nuna an samu canjin kashi 5.54 cikin dari daga N360/$ zuwa N381/$.

Irin wannan sauyin yana yin tasiri ga yan kasuwa da kamfanoni musamman wadanda suke siyo hajoji daga kasashen waje.

DUBA WANNAN: Ni ne nayi sanadin waƙar Jarumar Mata - Sunusi Oscar

3. Kudin shigo da kaya da zirga-zirga

Yan kasuwa da masu harkar shigo da kaya daga kasashen waje sun bayyana damuwarsau a kan wahalhalun zirga zirga da kudaden da ake biya wurin shigo da kaya musamman a tashohin Najeriya.

Masu ruwa da tsaki a bangaren tashohin jirgin ruwa suna koka wa da jinkiri da ake samu wurin tantance kayayyakinsu da kuma kudin gadi da suke biya wa kwantenoninsu.

Misali a nan, akwai wata kamfanin tsaro da ake biyan ta dalolin Amurka masu yawa domin samar da tsaro a tashan Legas.

An yi ikirarin cewa a kan biya wa kaya fiye da Naira 762,000 kuma kayan na iya shafe makonni a wurin ajiyar kafin a kammala tantance su.

4. Wasu tsirarun abubuwa

Baya ga batun annobar korona, rage darajar Naira, kudaden shigo da kaya akwai wasu abubuwa da ka iya shafar kasuwanci daya daga cikinsu kuma shine yadda mutane ke koma wa yin sayaya ta shafin intanet a maimakon zuwa kanti.

Shoprite ta bude kantin ta na farko a Najeriya a shekarar 2005 kuma tana da rassa 26 a jihohi takwas har da Abuja.

Kantin ta yi ikirarin cewa ta kulla alakar kasuwanci da kamfanoni da manoman Najeriya fiye da 300.

Sai dai a lokacin da kantin ke bude rassarsa a Najeriya ne lokacin da ake samun karuwar kantinan shafin intanet da mutane ka iya yin sayayya ba tare da sun tafi waje ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel