Da duminsa: Daya daga cikin alkalan babban kotun tarayya ya rasu

Da duminsa: Daya daga cikin alkalan babban kotun tarayya ya rasu

- Allah ya yi wa Mai shari'a Jude Okeke na babbar kotun tarayya da ke Abuja rasuwa

- Okeke ya rasu yana da shekaru 64 a duniya a asibitin kasa da ke Abuja

- An tattaro cewa yayi korafin ciwon kirji a kwanaki kadan da suka gabata kafin rudewar jikinsa

- Rasuwar Okeke ya rage yawan alkalan babbar kotun tarayya daga 35 zuwa 34

Mai shari'a Jude Okeke na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya rasu.

Alkalin mai shekaru 64 ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kafin rasuwar Mai shari'a Okeke, shine na tara mafi daraja a cikin alkalan babban kotun tarayya.

Ya kasance dan asalin karamar hukumar Idemili ta Kudu da ke jihar Anambra.

Da duminsa: Daya daga cikin alkalan babban kotun tarayya ya rasu
Da duminsa: Daya daga cikin alkalan babban kotun tarayya ya rasu Hoto: The Nation
Asali: UGC

An gano cewa yayi korafin ciwon kirji a kwanaki kadan da suka gabata kafin rudewar jikinsa.

Ya zama lauya mai zaman kansa a 1985 kuma ya hidimtawa kasa a shekarar gabanta.

KU KARANTA KUMA: Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba

Yayi aiki a matsayin lauya mai zaman kansa har zuwa lokacin da ya zama alkalin babbar kotun tarayya a 2007.

Rasuwarsa ya rage yawan alkalan babbar kotun tarayya daga 35 zuwa 34.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ta sanar da rasuwar tsohon manajan daraktanta, Dr Joseph Thlama Dawha.

Dr. Dawha ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, manajan bangaren hulda da jama'a, Dr. Jennie Obateru ya sanar a wata takarda a ranar Litinin da dare.

Manajan daraktan kamfanin, Malam Mele Kyari, ya nuna matukar damuwarsa a kan mutuwar farat daya da Dr. Dawha yayi, wanda shine manajan darakta na 16 na kamfanin.

Malam Kyari ya ce daukacin NNPC ta na jimami tare da ta'aziyyar mutuwar tsohon GMD Dawha.

Ya tabbatar da cewa ya taimaka wurin shugabanci tare da bada gudumawa a bangarorin ci gaba da kamfanin.

Ya bayyana mutuwar Dr. Dawha a matsayin babban rashi ga NNPC tare da Najeriya baki daya.

Dawha ne GMD na kamfanin tsakanin watan Augustan 2014 zuwa watan Augustan 2015.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng