Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara da Matarsa sun kamu da COVID-19

Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara da Matarsa sun kamu da COVID-19

- Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara ya kamu da cutar COVID-19

- Gwaji ya nuna Mista Kayode Alabi da Matarsa su da wannan cuta

- Kayode Alabi shi ne shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jihar

Yanzu nan mu ka samu labari cewa mai girma mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi, ya kamu da cutar COVID-19.

Jaridar The Nation ta ce sakamakon gwajin da ya fito ya nuna cewa Kayode Alabi da kuma matarsa, Misis Abieyuwa duk sun kamu da cutar.

Mai magana da yawun kwamitin yaki da annobar COVID-19 a jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya bada wannan sanarwa a yau ranar Talata.

Rafiu Ajakaye ya fitar da jawabi cewa:

“A jiya, 3 ga watan Agusta, 2020 ne aka yi wa mataimakin gwamnan Kwara kuma shugaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 a jihar Kwara, Kayode Alabi da mai dakinsa, Abieyuwa, gwajin COVID-19 bayan sun fara nuna alamun kamuwa da cutar.”

KU KARANTA: An hana sallar idi saboda COVID-19 a wasu Jihohi

Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara da Matarsa sun kamu da COVID-19
Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara
Asali: Twitter

Jawabin ya kara da: “Sakamakon gwajin ya nuna su na dauke da kwayar cutar. Magidantan su na nan kalau cikin koshin lafiya, kuma yanzu haka su na bin matakan da gwamnati ta gindaya kamar yadda ma’aikatan lafiyan gwamnati su ka bada shawara.”

Ajakaye ya ce ma’aikata sun fara laluben wadanda su ka hadu da wadannan Bayin Allah domin a dauki matakan da su ka dace na takaita yada cutar a jihar.

“An fara gaggawar laluben wadanda su ka samu alaka da magidantan a cikin kwanakin bayan nan, tare da yin gwaji da daukan duk wasu matakan kariya.”

Kwamitin ya rufe jawabi da cewa: “Gwamnati ta na yi wa magidantan fatan samun lafiya.”

A farkon makon nan ne gwamnatin jihar Kwara ta bada sanarwar cewa za a bude makarantu a ranar 5 ga watan Agusta, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel