Tambuwal ya saki fursunoni 17 a jihar Sakkwato

Tambuwal ya saki fursunoni 17 a jihar Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, ya saki fursunoni 17 da ke zaman cin sarka a wani mataki na gyara hali cikin babban gidan kaso da ke birnin Shehu.

An saki fursunonin masu kananan laifuka domin biyayya ga umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa gwamnatocin jihohi na rage cunkoso a gidajen gyara hali da ke fadin kasar.

Muhammadu Bello, hadimi na musamman ga gwamnan kan harkokin sadarwa da hulda da al'umma, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Mista Bello ya ce wannan karamci wani bigire ne na nauyin da gwamnatin jihar ta rataya a wuyanta na yi wa masu fursunoni masu kananan laifuka afuwa.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato
Asali: Twitter

Ya ce uku daga cikin fursunoni 17 da aka 'yantar sun aikata laifuka ne masu cin karo da dokokin kasa yayin da ragowar ke cin saraka sakamakon laifukan da suka aikata na yi wa dokokin jihar karan tsaye.

Ya kara da cewa, kwamishinan shari'a kuma lauyan koli na jihar, Suleiman Usman, shi ne ya shiga ya fita wajen ganin gwamnatin jihar ta bai wa fursunonin 17 damar shakar iskan 'yanci.

"Wannan afuwa da gwamnan ya yi wa fursunonin ta samo asali ne daga cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999," inji shi.

Ya kirayi fursunonin da aka yi wa afuwa da su nisanci ayyukan mugunta kuma su daukewa kawunansu kewa da ayyukan da zasu inganta rayuwarsu.

Ya ce lauyan koli na jihar ya kuma rarrabawa kowane daya daga cikin 'yantattun fursunonin nai dubu hamsin a matsayin kudin guzurin komawa gida.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kano za ta yi wa makarantun boko 528 feshin magani

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saki fursunoni 29 da ke zaman gidan gyaran hali na Dutsen-Goro a Kano.

Gwamnan da ya bayar da umurnin sakin fursunonin a yayin da ya kai ziyara gidan gyaran halin a ranar Juma'a, inda ya ce ya aikata hakan ne saboda murnar bikin babbar Sallah.

Ganduje ya ce an yi la'akari da irin laifukan da suka aikata da kuma alamun sauyin halayensu yayin zamansu a gidan gyaran halin.

Ya ƙara da cewa dalilin ziyarar shine don nuna wa fursunonin cewa gwamnati ta na sane da zamansu kuma suma mazauna jihar Kano ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel