Ku sadu da Attajirin Najeriya da zai mallaki kamfanin Shoprite

Ku sadu da Attajirin Najeriya da zai mallaki kamfanin Shoprite

Shoprite, kamfanin manyan shagunan siyayyan kayayyaki mafi girma a Afrka, ta sanar da yiwuwar siyar da mafi rinjaye na hannun jarinta a Najeriya a ranar Litnin.

A wani karin haske da ta yi, babbar kamfanin ta ce ta fara bin tsarin bugar da mafi rinjaye na hannun jarinta.

“Biyo bayan rokon iri daga masu hannun jari daban-daban, da kuma tsarin sashin auna shirye-shiryenmu a Najeriya, hukumar ta yanke shawarar fara shirin duba yiwuwar siyar da dukka, ko kuma mafi rinaye na hannun jarinta, a manyan katunanta na Najeriya,” ta ce.

Jaridar The Cable ta fahimci cewa akwai fafutuka da ake yi tsakanin kamfanoni uku na son kama mafi girman kaso na kamfanin.

Ku sadu da Attajirin Najeriya da zai mallaki kamfanin Shoprite
Ku sadu da Attajirin Najeriya da zai mallaki kamfanin Shoprite Hoto: The Cable
Asali: UGC

Persianas Nigeria Limited, wata kamfanin bunkasa kadarori, wacce take mallakar Tayo Amusan, itace ta fi samun karbuwa cikin masu saka farashin sayan kamfanin na Shoprite.

Amusan ya kasance biloniyan dan kasuwa wanda ke da hannun jari a fannin bunkasa kadarori. A wasu daga cikin kadarorinsa ne kantin Shoprite suke.

Amusan ya kafa Persianas a 1990. A 2004, ya kaddamar da The Palms. Biyo bayan nasarar da ya samu a The Palms a Lagas, sai ya samar da karin manyan shagunan siyayya a Enugu, Kwara, Ota da Ibadan.

Amusan ya jagoranci kamfanonin Najeriya da dama, ciki harda African Paints Nigeria Limited, kuma shine Shugaban kamfanin Resourcery Limited.

Sauran mutane biyu da ke zawarcin siyan kayayyakin sun kasance wasu kamfanonin bunkasa kadarorin amma suna da alaka da kasar waje, da kuma wata kamfani na Afrika ta Kudu tare da goyon bayan hukumar kudin fansho na Afrika ta Kudu.

KU KARANTA KUMA: 'Zama daram a Najeriya': Shoprite ta yi karin bayani a kan labarin janyewa daga Najeriya

Koda dai Amusan ne wanda ya fi soyuwa, sauran masu cinikin na ta kokarin ganin an sasanta.

Jaridar The Cable ta fahimci cewa yarjejeniyar zai hada da Shoprite ta ci gaba da rike manajojinta, sunanta, alamar kamfaninta, da kuma wajen shigo da kayayyakinta.

Kimanin shekaru 15 kenan da kamfanin ta fara aiki a Najeriya, inda ta bude kantinta na farko a Lagas a watan Disamba 2005.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel