Zaben Edo: Mataimakin shugaban majalisa da mambobi 3 sun juyawa Obaseki baya

Zaben Edo: Mataimakin shugaban majalisa da mambobi 3 sun juyawa Obaseki baya

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Mista Yekini Idiaye, tare da sauran wasu mambobin majalisar hudu sun bayyana goyon bayansu ga takarar Fasto Ize-Iyamu a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

'Yan majalisar na daga cikin mambobi 10 da aka rantsar a cikin watan Yuli na shekarar 2019 yayin da har yanzu ake jiran rantsar da sauran wasu 14.

A cewar 'yan majalisar, sun yanke shawarar zama a cikin APC saboda a karkashin inuwar jam'iyyar su ka ci zabe.

Kazalika, sun bayyana cewa ba zasu bi gwamnn jihar Edo, Godwin Obaseki, zuwa cikin jam'iyyar PDP ba.

Mambobin sun yi zargin cewa bangaren gudanarwa a karkashin jagorancin Obaseki ya wofantar da majalisa tare da hanata yin aiki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A baya Legit.ng ta wallafa rahoton cewa wasu 'yan daba da ake zargin suna goyon bayan dan takarar jam'iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, sun gwabza da 'yan dabar da ke goyon bayan gwamna Obaseki, dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Gungun 'yan dabar sun fafata a daura da fadar sarkin Benin, Oba Ewuare II, a ranar Asabar.

Zaben Edo: Mataimakin shugaban majalisa da mambobi 3 sun juyawa Obaseki baya
Gwamna Obaseki
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta yayin fafatawar 'yan dabar, lamarin da ya haifar da raunata jama'a tare da lalata ababen hawa.

Rikicin ya barke ne lokacin da gwamna Obaseki tare da sauran gwamnonin jam'iyyar PDP suka ziyarci fadar sarkin gabanin kaddamar da yakin neman zaben Obaseki a matsayin gwamnan jihar Edo a karo na biyu.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Gemade da su Dogara suka koma APC - Sakataren yada labaran jam'iyya

Wata majiya ta bayyana cewa rigimar ta balle ne bayan gwamnan da tawagarsa sun bar fadar sarkin, sannan an fi yiwa bangaren jam'iyyar PDP barna saboda magoya bayan jam'iyyar APC sun fisu yawa.

Majiyar ta kara da cewa magoya bayan PDP sun garzaya filin wasan tamaula na Ogbe, wurin taron jam'iyyar, inda suka nemi gudunmawar abokansu domin ramuwar gayya a kan magoya bayan jam'iyyar APC.

Majiyar jaridar Daily Trust ta sanar da ita cewa an raunata magoya bayan kowacce jam'iyya, sannan an lalata motoci.

Sai dai, daga bisani jami'an 'yan sanda sun kawo dauki tare da kwantar da rikicin.

Da yake magana a kan rikicin da aka yi a tsakanin magoya bayan APC da PDP, gwamna Obaseki ya gargadi magoya bayansa da su kasance masu zaman lafiya a duk inda suka samu kansu.

"Ba ma son zubar da jini."

"Kar ku dauki fansa amadadinmu"

"Burinsu shine su tsorata jama'a," a cewae Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel