Sai ‘Dan Kudu ya zama Shugaban kasa za ayi watsi da tsarin kama-kama - Inji AYPS

Sai ‘Dan Kudu ya zama Shugaban kasa za ayi watsi da tsarin kama-kama - Inji AYPS

Wata kungiya ta matasan yankin Arewa ta na marawa takarar shugaban kasa daga Kudancin Najeriya baya a zabe mai zuwa na 2023.

Kungiyar Arewa Youths for Peace and Security wanda aka fi sani da AYPS, ba ta tare da Mamman Daura, wanda ya ke da ra’ayin cancanta ta yi aiki a zaben 2023.

Shugaban AYPS, Alhaji Salisu Magaji, ya na ganin cewa idan mulki ya koma yankin Kudancin Najeriya ne za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Salisu Magaji ya fitar da jawabi ya ce, ko da su na ganin ya kamata ayi watsi da tsarin kama-kama kamar yadda Mamman Daura ya fada, amma hakan zai kawo matsala.

Duk da cewa Magaji ya na da ra’ayin a kyale cancanta da nagarta su yi aiki a zaben 2023, ya ce: “Matsayar mu ita ce Arewa ta marawa Kudu baya domin a zauna lafiya.”

“Domin samun daidaito, adalci da gaskiya, ya kamata shugaban kasa ya sake fitowa daga Kudancin Najeriya kafin a daina amfani da tsarin kama-kama.” Inji kungiyar.

KU KARANTA: Kudu ya kamata su fito da Shugaban kasa bayan Buhari - Babachir

Sai ‘Dan Kudu ya zama Shugaban kasa za ayi watsi da tsarin kama-kama - Inji AYPS
Mamman Daura a Landan
Asali: Twitter

AYPS ta ce: “Mu da ra’ayin cewa idan Arewa ta cigaba da mulki bayan Buhari ya kammala wa’adinsa, wannan zai shafi zaman lafiyar kasar, kuma zai rusa hadin-kai.”

“Shawarar mu ita ce, Arewa ta bada wuri mutumin Kudu ya gaji Buhari.” Matasan su ka ce ya zama dole yankin ya hakura da mulki a zabe mai zuwa.

“Daga nan a 2031, lokacin da Kudu sun yi mulki, za mu iya fara maganar cancanta da nagarta ba tare da la’akari da yankin da ‘dan takarar shugaban kasa ya fito ba.”

Ta ce zuwa wannan lokaci za ayi amfani ne da kyawun ‘dan takara da sanin aikinsa da nufin kawowa kasa cigaba, ba a rika kallon yankin da zai yi mulki ba.

Kungiyar ta ce a baya an yi haka a Masar inda Auwal Sadat ya rike kasar tare da danuwansa na jini Hosni Mubarak a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel