Jarumin Indiya, Amitabh Bachchan ya samu sauki daga cutar COVID-19

Jarumin Indiya, Amitabh Bachchan ya samu sauki daga cutar COVID-19

- Coronavirus: Amitabh Bachchan ya warke, ya bar Abishek a asibiti

- A watan jiya ne ‘Dan wasan mai shekara 77 ya shaidawa Duniya ya kamu

- Mista Amitabh Bachchan ya yi kwanaki 20 ya na jinya a wani asibiti

A ranar Lahadi mu ka ji cewa, jarumin fina-finan Indiya, Amitabh Bachchan, ya bar asibiti bayan ya yi fama da jinyar COVID-19 na tsawon makonni uku a gadon asibiti.

Abishek Bachchan wanda aka kwantar da shi tare da mahaifinsa watau Amitabh ya na kwance har yanzu a asibiti. Tauraron wasan kwaikwayon bai warke ba tukuna.

A makon jiya surukar, Mista Abishek Bachchan, Aishwarya Rai da ‘Diyarta Aaradhya su ka bar asibiti. Iyalin na Bachchan su na cikin wadanda COVID-19 ta kama a Indiya.

Bayan fitowarsa daga asibiti, Mista Amitabh Bachchan mai shekaru 77 ya yi magana a shafinsa na Instagram, ya ce gwajin da aka yi masa ya nuna kwayar cutan ya bar jikinsa.

Bachchan ya rubuta: “Na dawo gida. Zan killace kai na a dakina.”

Dattijon tauraron ya godewa iyalinsa da masoya da kuma malaman asibiti da su ka maida hankali kwarai da gaske wajen ganin ya samu lafiya.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi Tauraron Bollywood, Amitabh Bachchan

Jarumin Indiya, Amitabh Bachchan ya samu sauki daga cutar COVID-19
Amitabh Bachchan
Asali: Getty Images

‘Dinbin masoya sun taru a garin Kalkota domin taya Amitabh Bachchan murnar samun lafiya. Bachchan ya shafe shekaru fiye da 50 ya na fitowa a wasan kwaikwayo a Indiya.

Mista Bachchan ya samu sauki a daidai lokacin da aka ji labarin cewa ministan harkokin cikin gidan kasar Indiya, Amit Shah ya kamu da wannan mumummar cuta.

Sakatariyar kungiyar masoyan tauraron ta Amitabh Bachchan Fan Association, Sanjoy Patodiya, ta bayyanawa AFP cewa sun yi murnar samun labarin warkewar gwarzon na su.

Ana addu’ar Abishek Bachchan ya samu lafiya kamar yadda mahaifinsa da mai dakinsa duk su ka warke. Kawo yanzu alkaluma sun nuna COVID-19 ta kashe mutane 38, 135 a Indiya.

A halin yanzu an jera kwanaki biyar a jere, kullum sai an samu akalla sababbin mutane 50, 000 da aka samu dauke da Coronavirus a Indiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel