APC za ta ci gaba da mulkin Najeriya har bayan 2023 - Shugabar Mata
Shugabar mata ta kasa ta jam'iyyar APC, Stella Okotete, ta bayyana kyakkyawan fata da cewa jam'iyyar APC za ta ci gaba mulki a Najeriya har bayan shekarar 2023.
Misis Okotete, wacce mamba ce a kwamitin riko na jam’iyyar APC, ta bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da ta jagoranci tawagar da ta kai wa 'yan gudun hijira gudunmuwar kayan abinci a sansaninsu na Karamajiji da ke Abuja.
“Yunkurin mu na sake fasalin jam’iyyar APC a bayyane yake ga kowa. Muna samun sabbin mambobi kuma tsofaffin mambobinmu suna dawo mana.
"Mun sauya jam’iyyun saboda dalilai masu nagarta da ci gaba da gudanar da mulkin kasar nan sama da 2023."
"Don haka muke fatan jam'iyyar mu ta ci gaba da mulki har bayan 2023."

Asali: Facebook
"Zan iya shaida muku cewa jihohin da ba APC ke mulki ba duk za su dawo a hannun mu nan da zaben 2023. Ina mai tabbatar muku da cewa daga Jihar Edo za mu fara karba daga hannun PDP kwanan nan."
“Za mu dage wajen ganin jam'iyyar APC ta ci gaba da kasancewa a jihar Ondo, kuma zamu jajirce wajen kwato jihar Anambra daga hannun jam'iyyar adawa," inji shugabar matan ta Jam’iyyar APC.
Ta kara da cewa, a cikin wata daya kacal jam'iyyar APC ta sake farfadowa a karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.
KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Kogi
Okotete ta ce ta jagoranci tawagar ne zuwa sansanin 'yan gudun hijira domin bai wa nakasassu da zaurawa tallafin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa da na wake, katan-katan na taliyar yara (indomie) man gyada, garin kwaki da sauransu.
A karshe Misis Stella ta kara da cewa, gwamnatin APC za ta yi iyaka bakin kokorinta wajen gaggauta komawar 'yan gudun hijirar zuwa kauyuka da garuruwansu.
Stella ta fadi hakan ne yayin jaddada cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kwazo a fannin inganta sha'anin tsaro a kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng