Hanyoyi hudu da za a iya amfani da su don adana naman sallah

Hanyoyi hudu da za a iya amfani da su don adana naman sallah

Babbar Sallah Eid-ul-Kabir lokaci ne na murna da bukukuwa da kuma alummar musulmi ke yin layya da raguna, shanu da rakuma a kasashen duniya.

Hakan kuma na nufin cewa a kan samu nama sosai da ba dole bane a iya amfani da shi cikin kankanin lokaci don haka akwai bukatar a adana namar don gudun asara.

Musulmi su kan yi layya da rago ne domin girmama biyaya da mika wuya da Annabi Ibrahim ya yi ga umurnin Allah na yanka dan sa Ismail.

Amma kafin Annabi Ibrahim ya kai ga aikata hakan sai Allah ya samar da rago a madadinsa.

Hanyoyi hudu da za a iya adana naman sallah
Hanyoyi hudu da za a iya adana naman sallah
Asali: UGC

Galibi a kan kasa naman layya zuwa gida uku ne, kaso daya a bawa mabukata, daya a ajiye a gida sannan na karshen a raba wa yan uwan.

Shi dai nama ana iya ajiye shi na tsawon makonni ko watanni idan an san hanyoyin da za ayi amfani da shi.

Ga wasu hanyoyi da za a iya amfani da su domin adana nama kamar yadda Daily Trust ta wallafa:

1. Ajiye naman cikin firinji mai kankara

Ajiye nama cikin firinji mai kankara tana daga cikin hanyoyin adana nama na zamani a yanzu.

Kafin a saka nama a cikin naurar, sai a gyara naman a cire kashi domin ya rage yawa sannan a nade cikin leda ko ka saka cikin mazubi mai murfi.

Ka tabbatar iska baya shiga cikin mazubin ko ledan kafin ka saka.

2. Busar da nama

Domin amfani da wannan nau'in adanar, a kan yanka nama ya yi siriri sannan a dafa cikin ruwan zafi na tsawon mintuna 3 zuwa 5 don kashe kwayoyin hallita da ke naman.

Sai a ciro naman daga ruwan zafin a bari ya tsane. Daga nan kuma ana iya saka naman cikin naurar gashi wato oven amma kada a cika zafin ko kuma a ayi amfani itace a hada wuta wurin busar da naman.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

3. Amfani da gishiri

Idan mutum yana son amfani da gishiri wurin adana nama, sai ya tabbata ya barbade naman baki daya da gishiri sannan ya saka naman cikin leda ko kuma wani mazubi mai murfi da iska ba zai shiga ba.

Sai a ajiye naman a wurin mai sanyi ko cikin firinji amma kada a bari ya yi kankara.

Naman da aka yi wa irin wannan adanar yana iya yin watanni 3 zuwa 4 ko ba a saka cikin firinji idan bai yana cikin mazubin da iska baya shiga.

Lokacin da za ayi amfani da shi sai a wanke gishirin sannan a sarrafa naman.

4. Gasa naman

Domin adana nama ta wannan tsarin, yana da kyau a fara barbadawa naman gishiri domin tsaita lokacin da za a iya ajiyar naman.

Daga nan sai a turara naman na tsawon awa 7 da wuta mai zafin digiri Fahrenheit 145 ko digiri Fahrenheit na 155 na tsawon awa hudu.

Kada zafin ya wuce digiri Fahrenheit 155 domin wannan zafin zai dafa naman kuma ba hakan ake so ayi ba a nan.

Ana kuma iya amfani da itace wurin gasa naman amma shima ba wuta sosai za a cika ba kada naman ya dafu.

Naman da aka sarrafa ta wannan hanyar ana iya ajiyarsa na wata daya zuwa biyu cikin mazubi da iska ba zai shiga ba.

Amma binciken masanna kimiyya na zamani ya ce yawan cin gasashen nama na iya janyo ciwon daji wato kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel