Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun dawo kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, suna sace jama'a

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun dawo kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, suna sace jama'a

Masu garkuwa da mutane a ranar Alhamis sun dawo kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda ake zarginsu da kwashe matafiyan da ba a san yawansu ba.

Al'amarin garkuwa da mutane a kan babbar hanyar ya yi kasa tun bayan da aka haramta yawo tsakanin jiha da jiha sakamakon barkewar annobar korona a kasar nan.

Ganau ba jiyau ba, ya sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, al'amarin ya faru ne a kusa da kauyen Katari mintoci kadan bayan karfe tara na safiyar Alhamis.

Mohammed Lawan, wanda ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin, ya sanar da jaridar Daily Nigerian cewa masu garkuwa da mutanen sun tsare matafiya masu zuwa Kaduna wurin karfe 8:50 na safe.

"Bamu wuce nisan mita 250 a tsakaninmu ba lokacin da muka juya saboda mun hango su. Na ga mota kirar Honda CRV 98 da kofofinta a bude kuma babu kowa.

"Hakan yana nuna sun kwashe mutanen da ke cikinta ne inda suka yi cikin daji.

"A lokacin sai muka ji kararrakin harbin bindiga yayin da jirgin sama na sojojin ya iso yankin," Lawan yace.

Har a halin yanzu dai 'yan sanda basu yi martani a kan aukuwar lamarin ba.

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun dawo kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, suna sace jama'a
Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun dawo kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, suna sace jama'a. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda dan sanda ya dinga lalata da ni tun dare har asuba - Matar da ta take doka

A wani labari na daban, wani mutum dan asalin kasar Nijar wanda ake zargin yana samar wa da 'yan bindiga makamai ya sha mugun duka a hannun jama'a. An samu gawarsa a cikin wani rafi da ke karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

Kamar yadda wata takarda da ta fito daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce a ranar 26 ga watan Yuli, bayanai sun isa hedkwatar 'yan sandan jihar a kan gawa da aka gani ta wani dan asalin Nijar.

Ana zarginsa da samar da makamai ga 'yan bindiga, kuma an tsaresa ne a kauyen Diboni da ke karamar hukumar Gada a kan hanyarsu ta zuwa Zamfara.

"Ambaliyar ruwa ce ta tsaresa sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi. Wanda ake zargin ya bukaci jama'ar yankin da su t

aimaka masa don tsallake ruwa inda wani buhun da ke kan babur dinsa ya zama abun zargi. "Mazauna kauyen sun tirsasa shi inda suka nemi bude buhun amma wanda ake zargin ya ki amincewa da hakan.

"Ta karfin tsiya suka bude inda suka ci karo da makamai wanda hakan yasa mazauna kauyen suka masa duka tare da kona shi sannan suka saka shi a rafi," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel