Tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa ya kwashi dukiya ya gudu

Tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa ya kwashi dukiya ya gudu

Mamba mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu a majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume, ya ce wani tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa sannan ya kwashi dukiya ya gudu.

Sanata Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hirarsa da sashen Hausa na gidan radiyon BBC, kamar yadda lauya mazaunin Kano, Bulama Bukarti, ya wallafa a shafinsa na tuwita a ranar Laraba.

A cewar Bukarti, dukkan jama'ar da Boko Haram suka zalunta sun shaidawa BBC cewa basa goyon bayan tsarin gwamnati na sakin tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram zuwa cikin jama'a.

Wata mata da 'yan Boko Haram suka kashe mijinta a kan idonta ta yi korafin cewa rashin adalci ne ya sa gwamnati sakin yan ta'addar da suka kashe mijinta a yayin da har yanzu zafin kisansa ke sukar zuciyarta.

DUBA WANNAN: Ina garkuwa da mutane ne domin tara kudin sadaka - Malamin addini

Matar ta bayyana cewa har yanzu 'ya'yanta hudu ba sa iya zuwa makaranta saboda babu mai daukan nauyinsu kuma gwamnati ba ta basu wani tallafi ba, amma ta saki 'yan ta'addar da suka saka rayuwarsu cikin kunci.

Lauyan ya yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Buhari da ta saurari jama'a ta sake duba shirinta na sakin tubabbun mayakan Boko Haram.

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta ce tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram sun yi rantsuwa cewa zasu zama ma su biyayya ga gwamnatin tarayyar Najeriya kafin sakinsu.

DHQ ta bayyana cewa ta dauki tsawon makon guda ta na rantsar da tubabbun mayakan bayan kammala basu horon saisaita tunaninsu da kuma gyaran halayensu (DDR).

Tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa ya kwashi dukiya ya gudu
Tubabbun 'yan Boko Haram
Asali: Twitter

Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke jawabi a kan atisayen rundunar4 soji a tsakanin 9 ga watan Yuli zuwa 16 ga wata.

Janar Enenche ya bayyana cewa an bawa tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram horo daban - daban a karkashin atisayen 'SAFE CORRIDOR'.

Kazalika, ya ce sun barranta kansu da zama mambobin kungiyar Boko Haram bayan sun mika wuya.

A cewar Janar Enenche, bayan an kammala basu horo a sansanin Malam Sidi, tubabbun mayakan sun yi rantsuwa a gaban kwamitin alkalai mai mutane 11 cewa za su zama mutanen kirki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel