Magidanci ya yi wa matarsa mai juna biyu mugun dukan da ya kai ta lahira

Magidanci ya yi wa matarsa mai juna biyu mugun dukan da ya kai ta lahira

Ana zargin wani mutum mai shekaru 47 mai suna Olabode Oluwaseun da laifin yi wa matarsa mai dauke da juna biyu dukan da ya kai ta lahira.

An gano cewa Olabode ya bigi matarsa mai suna Blessing ne a ciki wanda yasa ta mutu tare da cikin.

An gurfanar da wanda ake zargin a kan laifi daya a gaban wata kotun majistare, sakamakon laifin da ake zargin ya aikata a ranar 3 ga watan Afirilu a gida mai lamba 56, yankin Oke-Agba da ke Akure.

An zargesa da dukan matarsa ta bangaren dama a cikinta wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta da dan dake cikinta.

Dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Uloh Goodluck, ya sanar da kotun cewa laifin abin hukuntawa ne a karkashin sashe na 319, sakin layi na 1 na dokokin laifuka na jihar Ondo.

Uloh ya ce, wannan shari'a ce ta kira kuma ya bukaci kotun da ta bada umarnin tsare Olabode a hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da za su samu shawara daga sashen gurfanarwa na jihar.

Lauyan Olabode, A. Ololike, bai soki bukatar adana wanda ake zargin ba a hannun 'yan sanda.

Alkali mai shari'a, N. T Aladejana, ya bada umarnin ci gaba da tsare Olabode a hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da za su samu shawara daga DPP.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Satumba.

Magidanci ya yi wa matarsa mai juna biyu mugun dukan da ya kai ta lahira
Magidanci ya yi wa matarsa mai juna biyu mugun dukan da ya kai ta lahira. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin rashawa: Gwamnan Bauchi ya zargi Dogara da yi masa sharri

A wani labari na daban, wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani na Florence Wathoni Anyansi, daya daga cikin masu shirin gidan BBNaija na wannan shekarar nan ya bai wa jama'a da yawa mamaki.

Budurwar ta bayyana yadda ta samu juna biyu duk da kuwa da budurcinta kuma bata taba lalata da kowa ba a lokacin da take shekaru 23.

A bidiyon da a halin yanzu ya karade kafafen sada zumuntar zamani, mahaifiyar yaro dayan ta bayyana cewa ta samu dan wani lokaci tare da saurayinta suna shafe-shafen juna.

Daga nan ne ya goga mazakutarsa a gabanta har ya fitar da maniyyi duk da kuwa bai shiga ko ina ba.

Wathoni ta ce bayan aukuwar lamarin ta daina ganin al'adarta amma bata dauka al'amarin da muhimmanci ba saboda ta san ba zai yuwu ta samu ciki ba bayan basu yi wani abun a zo a gani ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel