Ondo 2020: Akwai yiyuwar mataimakin gwamna zai sauya sheka mako mai zuwa

Ondo 2020: Akwai yiyuwar mataimakin gwamna zai sauya sheka mako mai zuwa

Akwai hasashen cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon Agboola Ajayi, zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a mako mai zuwa. Majiya mai tushe ta ce zai shiga jam'iyyar ZLP, wacce ita ce jam'iyya ta uku mai matukar karfi a jihar.

Ajayi ya fice daga jam'iyyar APC a watan Yuni, inda ya tsaya takara a zaben fidda gwani na PDP a watan Yuli, inda ya zamo na biyu da kuri'u 657.

Rahotanni sun yi nuni da cewa ya hadu da tsohon gwamnan jihar Olusegun Mimiko, inda suka tattauna kan yadda jam'iyyar ZLP zata bashi tikitin takara.

Idan har jam'iyyar ZLP ta ba Ajayi tikitin takara, to zata musanya sunansa da na Hon Rotimi Benjamin, wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Majiya daga jam'iyyar ZLP ta ce ana duba yiyuwar ba Ajayi tikitin takara ne la'akari da yawan kuri'un da ya samu a PDP duk da cewa ya shiga jam'iyyar a kurarren lokaci.

A baya bayan nan ne Ajayi ya ce shi da magoya bayansa zasu ci gaba da zama a PDP, amma a wata sanarwa ya ce har yanzu yana kan nazari zama ko ficewa daga jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Ina garkuwa da mutane ne domin tara kudin sadaka - Malamin coci

Ondo 2020: Akwai yiyuwar mataimakin gwamna zai sauya sheka mako mai zuwa
Ondo 2020: Akwai yiyuwar mataimakin gwamna zai sauya sheka mako mai zuwa
Asali: UGC

A wani labarin, rundunar 'yan sandan Nigeria a ranar Laraba ta gurfanar da wani tsohon malamin coci, Adetokunbo Adenokpo, bisa zarginsa da yin garkuwa da wani dan aike.

Bayan yin garkuwa da dan aikine, Mr Adenokpo ya boye shi a dakin da ke karkashin cocin, a Sagamu, jihar Lagos.

Jami'in hulda d jama'a na rundunar DCP Frank Mba, ya gurfanar da Adenokpo tare da wasu mutane 34 da ake zarginsu da laifuka daban daban, a shelkwatar rundunar da ke yaki da fashi da makami a Abuja, a ranar Laraba.

Malamin cocin ya ce ya yanke shawarar shiga harkar garkuwa domin tara kudaden da zai rabawa mabukata sadaka.

Ya ce duba da cewa bukukuwan babbar Sallah na gabatowa, ba shi da kudi, dole ya nemi kudin da zai sai kayayyaki kamar shinkafa, wake, rago d.s domin rabawa mabukata.

Malamin cocin ya ce shirin bayar da tallafin bai tsaya akan addinin kirista kawai ba, har da sauran addinai.

DCP Mba ya ce dan aiken Job Ekpe Jonathan, na aiki ne da kamfanin tura sakonni na Glory Master, ya shiga komar Adenokpo da tawagarsa ne a lokacin da ya kai wasu kayayyaki cocin.

Mba ya ce malamin cocin, wanda shine shugaban cocin Newlife Church of God da ke Sagamu, ya yiwa dan aiken allurar anesthesia domin galabaitar da shi don basu saukin daure shi.

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da bincike da kuma samun damar ceto Jonathan a inda aka daureshi, wani daki dake karkashin cocin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel