An cafke mutane 244 da suka yi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya
Mun samu rahoton cewa, hukumomin kasar Saudiya masu kula da aikin Hajji, sun samu nasarar cafke mutane fiye da 200 da suka yi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya.
A ranar Talatar da ta gabata ne aka kama mutane 244 yayin da suke kokarin satar hanyar shiga Masallacin Harami domin gudanar da aikin Hajjin bana ta ɓarauniyar hanya.
Kamar yadda Jaridar Saudi Gazette ta wallafa kuma kamfanin dillancin labaran kasar SPA ya ruwaito, tuni har an hukunta mutanen da suka yi yunƙurin aikata ba daidai ba.
SPA ta nakalto wani kakakin rundunar tsaron al'umma yana kiran mazauna Saudiya da su yi biyayya ga dokokin aikin Hajjin na bana sau-da-ƙafa.
Ya nemi mazauna Saudiyya da su kiyaye dokokin da cewa hakan shi zai taimaka wajen dakile yaduwar annobar korona wadda ta janyo asarar rayuka da dama a kasar.
Ya yi gargadin cewa kada wanda ya kuskura ya yi yunkurin gudanar da aikin Hajjin bana ba tare da ya samu mallaki takardun izini ba.
"Jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a ciki da kewayen Masallatan Harami domin tabbatar da an kiyaye waɗannan dokoki tare da kama masu ƙetara su," in ji shi.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Mahajjata sanye da takunkumin fuska sun fara aikin hajjin bana a ranar Laraba sai dai adadin su ba shi da yawa sakamakon annobar korona da ta tilastawa Saudiyya takaita adadin maniyyatan bana.
KARANTA KUMA: Babbar Sallah: A fadar Villa zan yi Sallar Idin bana - Buhari
Hajji dai yana daya daga cikin rukunan addinin musulunci da duk musulmin da Allah ya bawa iko ake son ya yi a kalla sau daya a rayuwarsa.
A sauran shekaru, ana iya cewa hajji na daya daga cikin taron addini da ke samun hallartar mutane da dama a duniya amma a bana lamarin ya canja.
Kimamin mutum 10,000 wanda dama mazauna kasar Saudiyya ne aka bawa ikon hallartar ibadar da aikin hajji a maimakon kimanin mutum miliyan 2.5 da suka yi aikin hajjin a bara.
Musulmi sun isa masallacin haramin na Makka inda suka fara gudanar da dawafi, wato zagayen Ka'aba suna adduoi kamar yadda wasu faifayen bidiyo na kasar Saudiyya suka suna.
An yi wa mahajjatan gwajin zazzabi sannan an killace su na kwanaki 14 a lokacin da suka isa kasar mai tsarki a karshen makon da ta gabata. An yi hakan ne don tantance masu dauke da cutar korona.
Kafafen watsa labarai na Saudiyya ya nuna yadda ake yi wa jakkunan mahajjata feshin maganin kashe kwayoyin cutar kuma wasu daga cikinsu an basu wani naura sun saka a hannunsu domin a rika sanin inda suke a kowanne lokaci.
Mahukunta a kasar ta Saudiyya sun zagaye dakin na Kaaba a bana inda suka ce ba za a bari mahajjata su rika shafansa ba domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
An kuma kara adadin asibitoci da asibitocin tafi da gidanka da motoccin daukan marasa lafiya a Makka domin kula da lafiyan cikin mahajjatan cikin idan bukatar hakan ta taso.
"Ba bu wata fargabar tsaro game a aikin hajjin amma an takaita adadin mahajjatan ne kawai domin dakile yaduwar annobar coronavirus," a cewar direktan tsaron alumma na Saudiyya, Khalid bin Qarar Al-Harbi.
An kuma hana kafafen watsa labarai na kasashen duniya damar zuwa daukan rahotanni yayin aikin hajjin na bana a yunkurin da gwamnatin kasar ta yi na tsaurara matakan tsaro.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng