Mijina yana kira na da Alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure

Mijina yana kira na da Alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure

- Matar aure ta nemi wata kotun gargajiya da ke Mapo da ta tsinke aurensu mai shekaru 12 da mijinta

- Ta bukaci sakin ne kan hujjar cewa mijin nata mai suna Segun na kwatanta ta da alade

- Mai shari'a Ademola Odunade, shugaban kotun tare da sauran alkalan biyu sun amsa bukatar matar tare da mallaka mata yaran da suka haifa da mijin nata

Wata matar aure mai yara uku da aka ambata da suna Oluwayemisi Ajakaye a ranar laraba, ta bukaci wata kotun gargajiya da ke Mapo, jihar Ibadan da ta tsinke aurensu mai shekaru 12 da mijinta.

Matar ta nemi takardar sakin ne kan hujjar cewa mijin nata mai suna Segun na kwatanta ta da alade.

Kamar yadda ta sanar da alkalin, ta ce: "Ya zargeni da bin maza duk da bana yi. A cikin shekarun nan, Segun baya barina cikin kwanciyar hankali.

"Ya zargeni da lalata da 'yan uwana, makwabta, 'yan kasuwa da kuma fasto."

Mijina yana kira na da alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure
Mijina yana kira na da alade, a taimaka a tsinke igiyar aurenmu - Matar aure Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Ta zargi Segun da kiran mahaifiyarta a waya tare da barazanar kasheta a gabanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma, wanda ake karar bai halarci zaman kotun ba balle ya kare kansa a game da laifukan da ake zarginsa.

Mai kare wanda ake karar ya ce an kai wa Segun takardar gayyata.

KU KARANTA KUMA: Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji

Mai shari'a Ademola Odunade, shugaban kotun tare da sauran alkalan biyu sun amsa bukatar matar.

Odunade ya bukaceta da ta rike dukkan yaransu uku tare da umartar Segun da ya dinga biyan mahaifiyar yaransa N15,000 a kowanne wata na kula da su.

A gefe guda, wani kotu na musamman a Legas da ke sauraron karar fyade da rigimar iyali ya yankewa wani ‘dan acaba mai shekaru 37 daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.

Jaridar Vanguard ta ce wannan kotu da ke zama a garin Ikeja ya samu Emmanuel Idoko da laifin keta alfarmar ‘diyar cikinsa mai shekara 12 da haihuwa.

Alkali Sybil Nwaka yayin da ya ke zartar da hukunci ya ce masu kara sun gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Mista Emmanuel Idoko ya aikata wannan laifi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng