Muna alfahari da salon shugabancinka - Gwamnonin APC ga Buhari

Muna alfahari da salon shugabancinka - Gwamnonin APC ga Buhari

- Gwamnonin APC na fadin kasar nan sun jinjinawa salon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kamar yadda gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya sanar a madadin gwamnonin, ya ce sun gamsu da wadatar tsaro da habakar tattalin arziki a kasar nan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa ya gamsu matuka da salon shugabancin Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar

Gwamnonin jam'iyyar APC sun ce suna farin ciki da salon shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A taron da suka yi da shugaban kasar ta yanar gizo a ranar Talata, gwamnonin sun ce shugaban kasar ya shawo kan matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

Sun bayyana yadda ya fitar da kasar daga halin rushewar tattalin arziki a 2016 da kuma annobar Coronavirus a matsayin wasu daga cikin nasarorin shugaban kasar.

"Muna alfahari da shugabancinka da kuma nasarorinka," Garba Shehu ya bayyana a cewar Atiku Bagudu a madadin sauran takwarorinsa.

Bagudu ne gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC.

A taron, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya da Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa duk sun halarta.

Muna alfahari da salon shugabancinka - Gwamnonin APC ga Buhari
Muna alfahari da salon shugabancinka - Gwamnonin APC ga Buhari. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

A watan Yuni, majalisar zartarwa ta kasa ta jam'iyyar APC ta sauke kwamitin gudanar da ayyuka wanda ke samun jagorancin Oshiomhole sakamakon rikicin shugabanci da ya yawaita.

An kafa kwamitin rikon kwaryar wanda ya samu jagorancin Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma tsohon sakataren kasa na jam'iyyar, don ya karba akalar mulkin jam'iyyar.

Shugaban kasar ya ce ya matukar gamsuwa da sauyin da ake samu a jam'iyyar.

"Ina matukar farin ciki da shugaban jam'iyyar da kuma ayyukan kwamitin sa. Yana yin duk kokarin da ya dace don karfafa jam'iyyar tare da tsara ayyukanta.

"Ina farin ciki da kokarinsa," Shehu ya bayyana kamar yadda Buhari yace.

"Ina farin cikin yadda suka san aikinsu a matsayin gwamnoni kuma suka gane hakkokinsu tare da basu fifiko," shugaban kasar yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel