Sojoji biyu sun riga mu gidan gaskiya a hadarin motar Zamfara

Sojoji biyu sun riga mu gidan gaskiya a hadarin motar Zamfara

Sojojin na musamman na Operation Hadarin Daji biyu sun mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon hatsarin motar da suka yi a hanyar Gusau zuwa Zaria a jihar Zamfara.

Hatsarin ya faru ne misalin karfe 11 na safiyar yau Talata a kauyen Damba da ke karamar hukumar Gusau babban birnin jihar mai nisan kilomita hudu daga garin Gusau, babban birnin jihar.

Wani cikin wadanda abin ya faru a idonsu, Anas Damba, ya shaidawa wakilin The Punch cewa sojojin suna tafiya cikin tawaga ne yayin da mota ta kwace wa daya daga cikinsu ya yi karo da mai motar haya Golf da ke zuwa da dayan hannun.

Sojoji biyu sun riga mu gidan gaskiya a hadarin motar Zamfara
Sojoji biyu sun riga mu gidan gaskiya a hadarin motar Zamfara. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

A cewar Anas, motar ta yi jifa da daya daga cikin sojojin inda wata mota da ke tawagar ta buge shi kuma ya mutu nan take a wurin.

"Sauran sojojin hudu kuma sun samu munanan rauni inda abokon aikinsu suka garzaya da su zuwa asibiti," in ji Anas.

Daya daga cikin sojojin da aka kai asibiti ya rasu a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau yayin da sauran ukun suna can suna karbar kulawa daga likitoci a asibitin.

Da ya ke zantawa da majiyar Legit.ng a wayar tarho, Kakakin Operation Hadarin Daji, Kwaftin Ibrahim Yahaya, ya ce baya Gusau a lokacin da abin ya faru amma an sanar da shi afkuwa abin bakin cikin.

"Ba na jihar Zamfara a halin yanzu. Ina garin Faskari ta jihar Katsina amma na samu labarin afkuwar abin bakin cikin," in ji Kakakin na Sojin.

A wani rahoton, mun kawo muku cewa, rikicin shugabanci, kabilanci da rashin nasarar kafa daular musulunci da kungiyoyin Boko Haram ta gaza yi ne dalilin da yasa mambobinsu ke mika wuya a cewar Sojojin Hadin Gwiwa na Kasa da Kasa, MNJTF.

A sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a, MNJTF ta ce 'yan ta'adda guda 47 ne suka ajiye makamansu suka mika wuya ga sojojinta da ke Tafkin Chadi da kewaye.

Timothy Antigha, Mai magana da yawun MNJTF da ke N’Djamena cikin wata sanarwa ya ce 'yan ta'addan tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Sector 1 ta MNJTF.

Ya ce daya daga cikin 'yan ta'adan da ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka kai hari a Banki, Fotokol, Gambarou Ngala, New Marte, Chikun Gudu da wasu wuraren ya bayyana damuwarsa kan rashin nasara a jihadin.

Mr Antigha, mai mukamin kwanel, ya ambaci cewa dan ta'addan da ya mika wuya ya ce sun gaza yin nasara saboda rikicin shugabanci da kwadayin abin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel