Yaki da cin hanci: An saki Abdulrasheed Maina daga gidan yari

Yaki da cin hanci: An saki Abdulrasheed Maina daga gidan yari

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa rahoton da ke tabbatar da cewa an saki Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho (PRTT) da tsohon shugaban kasa Jonathan ya kafa.

NAN ta bayyana cewa an saki Maina ne bayan ya shafe wata tara a tsare kamar yadda ta sanar da hakan a cikin rahoton da ta wallafa da yammacin ranar Talata.

A ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2019 EFCC ta gurfanar da Maina tare da dansa, Faisal, da wani kamfani; 'Common Input Property and Investment Ltd', a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Da ya ke tabbatar da hakan yayin hirarsa ta wayar tarho da NAN a ranar Talata, Adeola Adedipe, lauyan Maina, ya bayyana cewa an saki Maina da yammacin ranar Litinin bayan ya kammala cika ka'idojin samun 'yanci.

Lauya Adipe, wanda ke aiki a karkashin ofishin babban lauya Ahmed Raji (SAN), ya ce tun ranar 24 ga watan Yuli ya kamata a saki Maina amma wasu 'yan al'amura suka kawo tsaiko zuwa ranar 27 ga watan Yuli.

Da ya ke amsa tambaya a kan dalilin da yasa aka cigaba da tsare Maina bayan mai shari'a, Jastis Abang, ya sassauta sharudan bayar da belinsa a ranar 29 ga watan Yuni, sai lauyan ya ce: "an dan samu tsaiko wajen bin wasu hanyoyi da ka'idojin aiki."

Sai dai, Lauyan ya musanta cewa jami'an gwamnati sun kawo tsaiko da gan-gan domin ramuwar gayya a kan Maina.

Kazalika, Afam Osigwe, wani lauya daga cikin tawagar lauyoyin da ke kare Maina, ya tabbatar da cewa Maina ya koma gida cikin iyalinsa tun yammacin ranar Litinin.

Yaki da cin hanci: An saki Abdulrasheed Maina daga gidan yari
Abdulrasheed Maina a kurkuku
Asali: UGC

Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2019, kotu ta bayar da belin Maina, amma rashin cika sharudan bayar da shi beli suka sa aka cigaba da tsare shi a kurkuku kafin daga bisani lauyoyinsa su roki a sassauta sharudan belin.

Alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya amsa da rokon lauyoyin inda ya rage yawan sanatoci da zasu karbi belin Maina zuwa guda daya yayin wani zamana kotu a ranar 28 ga watan Janairu, 2020.

DUBA WANNAN: Mamman Daura ya shawarci 'yan Najeriya a kan zaben dan takarar shugaban kasa a 2023

Kazalika, ya rage adadin kudin belin Maina daga biliyan daya zuwa miliyan N500. Sauran sharudan bayar da belin Maina sun hada da mallakar kadara da kudinta bai gaza miliyan N500 ba a unguwar Asokoro, Maitama, Wuse II, da wasu sassan birnin Abuja.

Tilas duk Sanatan da ya karbi belinsa ya ke raka shi kotu duk lokacin da za a zauna.

Daga bisani Maina ya sanar da kotu cewa mamba mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, ya amince zai tsaya masa a matsayin wanda zai karbi belinsa a hannun kotu.

Maina, wanda ke fuskantar tuhumar cin hanci a gaban kotu, ya bayyana hakan ne ta bakin lauyansa, Joe Kyari Gadzama (SAN), yayin zaman kotu na ranar Talata, 23 ga watan Yuni, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel