Kotun daukaka kara ta yi fatali da karar Dino Melaye, ta jaddada nasarar Adeyemi
Kotun daukaka kara a birnin tarayya Abuja a ranar Talata ta yi watsi da karar da Sanata Dino Melaye ya shigar na kallubalantar nasarar Sanata Smart Adeyemi a matsayin wanda ya lashe zaben sanata ta mazabar Kogi ta Yamma.
Alkallan uku dukkansu sun amince a kan watsi da dalilai bakwai da aka yi laakari da su yayin watsi da daukaka karar ta Melaye.
Kotun ta jaddada hukuncin da Kotun Zaben Majalisa da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Yunin 2020 wacce ta tabbatar da nasarar Adeyemi kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta sanar.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi
Kazalika, kotun wacce ta farko ta yi watsi da bukatar da Adeyemi ya gabatar mata ta umurci wanda ya daukaka karar wato Melaye ya biya Adeyemi N50, 000.
Ku saurari cikaken rahoton ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng