Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid

Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid

A yayin da rashin tsaro ke kara tsamari a kasar, sanata a jamhuriya ta biyu, Dr. Junaid Muhammad ya bayyana cewa matukar shugabannin tsaron kasar nan suka ci gaba da zama a kan kujerunsu, akwai yuwuwar babban al’amari ya faru da kasar nan.

Dr Junaid ya ce hukumar soji "wata ma’aikata ce da ke da dokoki masu yawa kuma yin watsi da wadannan dokokin ga kowacce gwamnati na iya jefa ta a wani mugun hali."

A kalamansa, “Yan Najeriya na kallon hauhawar rashin tsaro a kasar nan kuma a koyaushe gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari suke dora wa laifi.

“Ba suna yin hakan bane saboda basu son shugaban kasar, amma suna yin hakan ne don haka ne ya dace. A kowacce kasa, babban aikin gwamnati shine bada kariya ga rayukan ‘yan kasa, dukiyoyinsu da martabarsu.

Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid
Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Wannan hakkin kuwa ya rataya ne ga wadanda ke shugabancin. A yau, Buhari, jam’iyyarsa, abokansa ko ‘yan uwansa da ke mulkin kasar nan ‘yan Najeriya ke dora wa laifi.

“A saboda wannan hikimar ne jama’a suka zabi wakilansu. Na san cewa majalisar dattawa sun mika bukata ga Buhari da ya sallami wadannan shugabanni sojin da suka kasa bada kariya a kasar nan.

“Amma kuma, har yanzu shugaban kasar bai yi martani a kan hakan ba. Abun takaicin shine yadda kakakinsa yace basu da wata matsala da shugabannin rundunar sojin.

“Toh idan kuwa haka ne, akwai babbar matsala a gabanmu tare da babbar annoba da ke kunno kai. Majalisar dattawa bata iya juya shugabannin tsaro sannan kuma shugaban bashi da hurumin kin jin maganar zababbu.

“Barin shugabannin tsaron nan tare da dora wa dukkan wanda ya kalubalancesu laifi zalunci ne. A bayyane yake shugabannin tsaron basu iya yin komai banda karbar makuden kudade da suke yi.

KU KARANTA KUMA: Idan kun isa ku ce kule ku gani a kan yaki da rashawa - Buhari ya yi wa PDP martani

“A matsayin hukumar sojin na ma’aikata mai zaman kanta, dole ne a kula da ita. Kula da ita kuwa yana nufin kiyaye dukkan dokokinta da ya hada da diban aiki, horarwa, Karin girma da yi wa wadanda ya kamata ritaya.

“A wannan lokacin da gwamnatin ta yanke shawarar watsi da dukkan dokokin, toh kuwa dole kasar nan ta fuskanci wata babbar matsala a nan gaba kadan.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel