Abba gida-gida ya maka Ganduje a kotu

Abba gida-gida ya maka Ganduje a kotu

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano, a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya maka gwamna Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya.

A wannan karon, ba zargin magudin zabe bane, zargi ne na daban ya kai su gaban kotun.

Abba gida-gida ya shigar da kara ne mai kalubalantar matakin da Ganduje ya dauka na mallakawa wasu sanannun 'yan kasuwa, mamallakan kamfanonin Mudatex da El-Samad babban otal na Daula.

Ba nan kadai gwamnan ya tsaya ba, ya mallaka musu gagarumar tashar Shahuci da ke cikin birnin Dabo.

Lauyan Abba Kabir Yusuf, Barista Bashir Yusuf, ya bayyana cewa hakan ya yi karantsaye ga tsarin kundun tsarin mukin kasar nan da ya yi magana a kan hakkokin mallakar kasa ko filaye.

Amma kuma, daga bangaren gwamnatin jihar, ya ce ba su san da labarin shigar da wannan karar ba.

Hakazalika, lauyan Abba gida-gida ya sanar da kotun cewa akwai bashi don gina titin jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki da gwamnatin ta ke yunkurin ciyowa daga China.

Ya tabbatar da cewa karbo wannan bashin zai jefa jihar Kano acikin halin ragargajewar tattalin arziki.

Ammam kuma lauyan Ganduje wanda shine antoni janar, kuma kwamishinan sharia'a na jihar kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko alamu babu na kamshin gaskiya a wadannan labaran.

Abba gida-gida ya maka Ganduje a kotu
Abba gida-gida ya maka Ganduje a kotu. Tashar Shahuci. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda na samu ciki da budurcina duk da ban taba jima'i da kowa ba - Budurwa

Ya bayyana cewa, an bai wa kamfanin H and I kwangilar gina sabuwar tashar zamani ta Shahuci ne don yin shaguna wadadan za a siyarwa 'yan kasuwa kamar yadda aka yi a kasuwar Dangauro da ke babban titin Zaria a Kano.

Ya kara da cewa, titin jirgin kasa kuwa tsohon aiki ne domin sai da gwamnatin jihar Kano ta samu amincewar gwamnatin tarayya kafin kasar China ta amince da bayar da bashin.

Barista Musa Lawan ya ce otal na Daula shi ma kwatankwacin hadin guiwa da gwamnatin Kano ta shiga da sauran kamfanoni ne amma ba ta mallakawa kowa shi ba.

Barista Lawan ya kara da cewa shi kuwa otal na Daula, hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin Kano da sauran kamfanonin amma babu wanda ta mallakawa.

Kamar yadda yace, hasalima tana duba yuwuwar bai wa masu sha'awar zuba hannayen jari dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel