Shawara kawai nake ba Buhari, ba juyashi nike ba - Mamman Daura ya yi maganarsa na farko na alakarsa ba gwamnatin Buhari

Shawara kawai nake ba Buhari, ba juyashi nike ba - Mamman Daura ya yi maganarsa na farko na alakarsa ba gwamnatin Buhari

Alhaji Mamman Daura, babban Amini kuma dan'uwan shugaba Muhammadu Buhari ya yi maganarsa ta farko kan alakarsa da gwamnatin shugaban kasa.

Daura ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Hausa, The Cable ta ruwaito Jaridar Vanguard da cewa.

Mamman Daura ya ce shawara kawai yake baiwa shugaban kasa, amma ba juyashi ba.

An dade an yada jita-jitan cewa Mamman Daura ne shugaban miyagun da ke hana ruwa tafiya a gwamnatin Buhari saboda suke tafiyar da komai.

A maganarsa ta farko kan alakarsu, ya ce ba tilastawa Buhari bin shawararsa.

A cewarsa, "Ba zaka iya wa gwamnatin haka ba."

Ya ce ya kan ziyarci Buhari kuma ya bashi shawara inda shi (Buhari) ya bukaci hakan.

Shawara kawai nake ba Buhari, ba juyashi nike ba - Mamman Daura ya yi maganarsa na farko na alakarsa ba gwamnatin Buhari
Mamman Daura
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC

Rahotan ya ruwaito Daura da cewa: "Mahaifina ne dan farkon mahaifiyarsu. Buhari ne dan auta,"

"Haka ne ina ziyartanshi. Ina bashi shawara, amma idan ya bukata. Amma ban zuwa can dan kaina kuma ince sai anyi kaza da kaza. Ba zaka iya wa gwamnatin haka ba."

Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta kasance tana adawa da Daura da iyalinsa.

A Oktoban 2019, bidiyo ya bayyana a yanar gizo da daya daga cikin 'yayan Mamman Daura, Fatima, ta saki a kafafan sada zumunta.

Aisha Buhari ta yi ikirarin cewa iyalan Mamman Daura sun hana ta shiga wani daki a fadar shugaban kasa.

Tun lokacin da Buhari ya hau mulki Mamman Daura da iyalansa ke zama a fadar shugaban kasa.

Bayan wa'adin Buhari na farko, Mamman Daura da iyalansa suka daina zama a fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel