Kwangiloli: Ministan N/Delta ya na neman ci mana mutunci – inji Majalisar Dattawa

Kwangiloli: Ministan N/Delta ya na neman ci mana mutunci – inji Majalisar Dattawa

A ranar Litinin majalisar dattawan Najeriya ta bayyana zargin da Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya jefe ta da su a matsayin neman ci mata mutunci.

Majalisar dattawan ta yi magana ne ta bakin shugaban kwamitin da ke kula da korafi, Sanata Ayo Akinyelure wanda ya ce zargin ba komai ba ne face kanzon kurege na kin-karawa.

Ayo Akinyelure ya ke cewa kwangilolin da Ministan ya ke ikirarin NDDC ta ba Sanatocin kasar ba ayyukan ma’aikatar ba ne, ya ce kwangilolin mazabu ne da ‘Yan majalisa su ka saba yi.

A cewar Ayo Akinyelure, an sa wadannan ayyuka na mazabu a cikin kasafin kudin Najeriya don haka takwarorinsa ba su karbi sisin kobo wajen yin wadannan ayyuka ba.

“Yadda gaskiya ta ke shi ne Sanatoci wakilan mutane ne, maganar Akpabio yunkurin cin mutunci ne wanda ba zai samu karbuwa a ko ina a Najeriya ba, mu na da damar cusa aiki a kasafin kudi.”

Sanata ya cigaba da cewa: “Ana raba mana ayyuka wanda ake bada su a hannun ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su ke yin wannan aiki.”

KU KARANTA: Binciken badakalar NDDC ya sa Dogara ya tafi Jam’iyyar APC – Bala

Kwangiloli: Ministan N/Delta ya na neman ci mana mutunci – inji Majalisar Dattawa
Sanata Godswill Akpabio Hoto: Majalisar Dattawa
Asali: UGC

“Wasu daga cikinmu daga yankin Neja-Delta za mu iya lallabawa mu nemi a kai kwangiloli mazabunmu. Wannan ba ya nufin an ba Sanatoci kudin da za ayi aikin. Ba mu taba kudi, mu na dai neman a kai ayyuka zuwa yankunanmu.”

“Shi Akpabio tsohon Sanata ne. Bai sa an kai ayyukan biliyoyin kudi zuwa mazabarsa ta hannun NDDC ba? Idan har ya yi haka, kuma ya ce an biya shi kudin aiki, magana ce ta wani kamfani ya yi ci kwangilar.”

Don haka ne majalisar ta ce maganar Ministan shafa-labari shuni ce, kuma kwamitinsu zai duba batancin da Akpabio ya ke kokarin jawowa ‘Yan majalisa domin daukar mataki.

Shugaban kwamitin harkar Neja-Delta a majalisa, Sanata Peter Nwaoboshi ya musanya zargin karbar kwangiloli 53 a ma’aikatar a 2018. A wani jawabi da ya fitar, ya kalubalanci Ministan.

Nwaoboshi ya nemi Akpabio ya aikawa hukumomin da ke yaki da rashin gaskiya bayanin kwangilolin da ya samu idan har Ministan ya tabbatar da abin da ya ke fada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng