Mamman Daura ya musanta cewa shi ke 'juya' Shugaba Buhari

Mamman Daura ya musanta cewa shi ke 'juya' Shugaba Buhari

Daya daga cikin makusantan Shugaba Muhammadu Buhari, Mamman Daura, ya musanta ikirarin da wasu ke yi na cewa shi ke fada wa Shugaba Buhari yadda zai tafiyar da harkokin mulki a kasar.

Tun bayan da Shugaba Buhari ya dare kan mulki a shekarar 2015, rahotanni da dama da aka wallafa sunyi ikirarin cewa Daura yana daga cikin tsirarin mutanen da ake yi wa lakabi da 'cabal' da aka ce su ke juya akalar gwamnatin Buhari.

Amma, a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, 28 ga watan Yuli, Daura ya ce shawara kadai ya ke bawa Shugaba Buhari amma ba ya tilasta masa ra'ayoyinsa ko fada masa abinda zai yi.

Mamman Daura ya musanta cewa shi ke juya Shugaba Buhari
Mamman Daura ya musanta cewa shi ke juya Shugaba Buhari
Asali: Twitter

Da aka tambaye shi dangantar da ke tsakaninsu da Shugaba Muhammadu Buhari, ya amsa da cewa Shugaban kasar kawunsa ne.

DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

"Mahaifi na shine na farko a wurin mahaifiyarsu. Buhari shine auta," in ji shi.

Da aka tunatar da shi rahotanni da ke cewa shi da Buhari sun taso tare kuma tun lokacin suna tare, ya ce, "Eh... wanan gaskiya ne." in ji shi.

Da aka masa tambaya kan cewa ko yana gana wa da Shugaba Buhari domin bashi shawarwari a kan harkokin da ke faruwa a Najeriya, Mamman Daura ya bayar da amsa kamar haka.

"Eh, na kan ziyarce shi domin in gaishe shi. Na kan bashi shawara amma idan ya tambaya ... Amma bana zuwa domin kashin kai na in dage cewa sai na tilasta masa wani abu. A'a. Ba a yi wa gwamnati haka."

Da ya ke tsokaci a kan bangaren kasar da ya kamata ta karbi mulki, ya ce yanzu lokaci ne 'yan kasar za su hada kai su zabi wanda ya fi cancanta.

"Wannan karba karbar anyi ta sau daya, sau biyu har sau uku ... Zai fi dacewa kasar ta hada kai wuri guda... Kamata ya yi a zabi wanda ya fi cancanta ba wai wanda ya fito daga bangare kaza ba," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel