Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

- Wasu fusatattun mambobin jam'iyyar APC sun yi barazanar sauya sheka kafin zuwan 2023

- Mambobin karkashin inuwar kungiyar APCPF sun ce an waresu yayin yin nade-nade a gwamnatin tarayya

- Akeem Akintayo, shugaban kungiyar, ya ce Buhari zai gane kuskuren da ya tafka na kin sakawa wadanda suka sha wuya wurin kafuwar jam'iyyar

Wani rahoto da jaridar The Sun ta ruwaito na bayyana cewa wasu 'ya'yan jam'iyyar APC a karkashin kungiyar kwararru ta jam'iyyar (APCPF), suna barazanar barin APC dukkansu idan har jam''iyyar ta ci gaba da kin saka su cikin nade-naden da take yi.

Legit.ng ta gano cewa, kungiyar ta kunshi kwararraru a fannin daban-daban wadanda suka yi rijista da jam'iyyar kuma suna goyon bayanta.

Shugaban kungiyar na kasa, Akeem Akintayo, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a sakateriyar jam'iyyar da ke Abuja a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2020.

Ya tunatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa, akwai kalubalen da za su iya fuskanta matukar jam'iyyar bata iya sakawa wadanda suka sha wuya wurin gininta.

"Siyasa ra'ayi ce kuma akwai dadi idan ka biya wanda ya yi maka aiki. A saboda haka ne muke kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya inganta masu biyayya ga jam'iyyar ta hanyar tallafa musu.

"Ya duba wadanda suka kafa jam'iyyar. Akwai babbar matsala a jam'iyyar nan saboda wadanda suka wahalar wa jam'iyyar basu tsintar komai.

Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili
Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda na samu ciki da budurcina duk da ban taba jima'i da kowa ba - Budurwa

"Muna ci gaba da kira ga shugaban kasa a kan ya bai wa wadanda suka kafa jam'iyyar nan tare da goyon bayansa mukamai. Muna ganin tamkar an ware mu duk da kokarin da muka yi wa jam'iyyar.

"Idan hakan bata faru ba, bamu da wani abu da zamu yi da ya wuce mu bar jam'iyyar kafin zuwan 2023," kungiyar ta ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel