An yanke wa fastoci biyu shekaru 26 a gidan kaso saboda satar N32m

An yanke wa fastoci biyu shekaru 26 a gidan kaso saboda satar N32m

Mai sharia F.N. Azinge na Babban Kotun Jihar Delta da ke zamanta a Otor-Udu ya yanke wa wasu fastoci biyu Fastor Glory Okeoghene Aberefa da Reverend Vincent Okpogo hukuncin zaman gidan kaso saboda sata.

An yanke wa Fasto Glory Okeoghene Aberefa hukuncin shekaru 16 yayin da shi kuma Reverend Vincent Okpogo aka yanke masa hukuncin shekaru 10 saboda satar Naira miliyan 32.

Sanarwar ta hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta fitar ya ce an yi karar fastocin tare da kamfaninsu Mustard Seed Micro Investment Limited, a ofishin hukumar da ke Benin inda ake tuhumarsu da aikata laifuka 16 masu alaka da sata da hadin baki.

An yanke wa fastoci biyu shekaru 26 a gidan kaso saboda satar N32m
An yanke wa fastoci biyu shekaru 26 a gidan kaso saboda satar N32m. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Wadannan laifukan sun saba wa sashi na Section 516 da 390 (9) na Criminal Code, CAP 21, Vol 1, na dokar jihar Delta ta shekarar 2006.

DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

Lauyoyin hukumar EFCC karkashin V. O. Agbaje and K. U. sun maka su a kotu ne sakamakon zarginsu da aka yi da satar kudi N32,516,620.00.

Wanda aka yi karar na farko, Fasto Aberefa an yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru 16 yayin da mutum na biyu Reverend Okpogo shima shekaru 16 aka yanke masa.

Idan ba a manta ba dama wadanda aka yanke wa hukuncin suna gidan kaso bayan yanke musu hukuncin zaman shekaru 17 da Babban Kotun Tarayya da ke Asaba da Babban Kotun Jihar Delta suka yi.

Mai sharia Azinge ya ce sabon hukuncin da aka yanke musu zai fara aiki da zarar sun kammala shekaru 17 da aka yanke musu a baya.

Masu laifin sun fada cikin rikici ne yayin da suka bude kamfanin hada hadar kudi mai suna Mustard Seed Micro Investment Limited inda suka rika damfarar mutane miliyoyin naira.

A wani labarin kun ji cewa Hukumar Yaki Da Rashawa, EFCC, reshen Jihar Gombe ta yi nasara a kan Samuel Bulus Adamu a gaban Mai sharia N.I. Afolabi na Babban Kotun Tarayya da ke Gombe.

Kotun ta same shi da aikata dukkan laifuka bakwai da EFCC ta ke zarginsa da aikatawa kana ta yanke masa hukuncin shekara 31 a gidan gyaran hali kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sanarwar da EFCC ta fitar yace, an fara gurfanar da tsohon shugaban karamar hukumar ta Shongomne a ranar 9 ga watan Maris na 2015 kan laifuka masu alaka da damfara, almundahar kudi da cuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel