Yanzu: Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen Tinubu, Fashola da Osinbajo

Yanzu: Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen Tinubu, Fashola da Osinbajo

- Shugaban kasa Buhari ya amince da sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen Tinubu, Fashola da Osinbajo

- Buhari ya amince da sanya sunayen zakakuran 'yan Nigeria ne kawai saboda gudunmowar da suka bada wajen bunkasa rayuwar al'umma

- Tun a watan Yuni, aka sa sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babbar tashar layin dogo da ke Agbor, babbar tashar jirgin Itakpe-Warri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sanyawa filayen jiragen kasa na Lagos-Ibadan, dana Itakpe-Ajaokuta-Wari, sunayen wasu zakakuran 'yan Nigeria, a cewar ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Hadimin shugaban kasar, Tolu Ogunlesi, ya bayyana hakan a ranar Litinin a shafinsa na Twitter.

A cewar Ogunlesi, an sanyawa sunan tashar jirgin saman Apapa sunan Bola Ahmed Tinubu, yayin da tashar Agege aka sa sunan ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.

Wasu daga cikin wadanda aka sanya sunayensu a tashoshin jiragen sun hada da Lateef Jakande (tashar jirgin Agbado), mataimakin shugabn kasa Yemi Osinabajo (tashar Kajola).

Sai kuma Funmilayo Ransome-Kuti da aka sa sunansa a tashar Papalanto.

Tun a watan Yuni, shugaban kasa Buhari ya amince da sa sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babbar tashar layin dogo da ke Agbor, babbar tashar jirgin Itakpe-Warri.

A cewar sanarwa daga ma'aikarar sufuri, Buhari ya amince da sanya sunayen zakakuran 'yan Nigeria ne kawai saboda gudunmowar da suka bada wajen bunkasa rayuwar al'umma.

Ga jerin sunayen 'yan Nigeria da aka sa sunansu a tashoshin jiragen kasa da ke fadin kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta

Yanzu: Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen Tinubu, Fashola da Osinbajo
Yanzu: Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen kasa sunayen Tinubu, Fashola da Osinbajo
Asali: Depositphotos

Daga Lagos zuwa Ibadan, har zuwa tashar jirgin ruwa ta Lagos da ke kusa da babbar tashar layin dogo ta Apapa.

Bola Ahmed Tinubu (tashar jirgin kasa ta Apapa)

Mobolaji Johnson (tashar jirgin kasa ta Ebute Metta)

Babatunde Raji Fashola (tashar jirgin kasa ta Agege)

Lateef Jakande (tashar jirgin kasa ta Agbado)

Prof. Yemi Osinbajo (tashar jirgin kasa ta Kajola).

Funmilayo Ransome-Kuti (tashar jirgin kasa ta Papalanto)

Prof. Wole Soyinka (tashar jirgin kasa ta Abeokuta)

Aremo Segun Osoba(tashar jirgin kasa ta Olodo)

Chief Ladoka Akintola (tashar jirgin kasa ta Omio-Adio)

Chief Obafemi Awolowo (tashar jirgin kasa ta Ibadan)

Chief Alex Ekwueme (tashar jirgin kasa ta Operation Control)

Daga tashar jirgin kasa ta Itakpe-Ajaokuta/Aladja-Warri

Alhaji Adamu Attah (tashar jirgin kasa ta Itakpe)

Dr. Olushola Saraki (tashar jirgin kasa ta Ajaokuta)

Admiral Augustus Aikhomu (tashar jirgin kasa ta Itogbo)

Brigadier General George Innih (tashar jirgin kasa ta Agenebode)

Anthony Eromosele Enahoro (tashar jirgin kasa ta Uromi)

Chief Tom Ikimi (tashar jirgin kasa ta Ekehen)

Brig. Gen. Samuel Osaigbovo Ogbemudia (rtd) (tashar jirgin kasa ta Igbanke)

Goodluck Ebele Jonathan (tashar jirgin kasa ta Agbor Station)

Brigadier General David Ejoor (tashar jirgin kasa ta Abraka)

Micheal Ibru (tashar jirgin kasa ta Opara)

Alfred Rewane (tashar jirgin kasa ta Ujevwu)

Vice Admiral Mike Akhigbe (tashar jirgin kasa ta Railway Village, Agbor)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel