An samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 5 baya - Buratai

An samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 5 baya - Buratai

Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Najeriya (COAS), Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce an fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yanzu idan aka kwatanta da shekarar 2014.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaje wurin wasu sojoji da suka samu raunuka a jihar Kaduna.

Kalaman na Buratai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu mutane ke ganin cewa Najeriya na fuskantar babbar barazanar tsaro sakamakon yawaitar hare-haren 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram, musamman a arewacin Najeriya.

Manema labari sun halarci asibitin rundunar soji da ke Kaduna domin shaida yadda ake duba lafiyar dakarun soji da suka samu raunuka yayin atisaye daban - daban a fadin kasa.

Da yake bayyana jin dadin kasancewa tare da sojojin da suka samu raunuka, Buratai ya bawa sojojin tabbacin cewa kishinsu da kokarinsu na tabbatar da an samu tsaro a kasa ba zai fadi kasa a banza ba.

An samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 5 baya - Buratai
Buratai yayin ziyarar sojojin da suka samu raunuka
Asali: Twitter

"Na yi matukar farin cikin sake ganinku, na hadu da wasu a cikinku a filin yaki kuma na ga irin kwarfin gwuiwar da kuke da shi. Wannan shine farashin da kuka biya don kishin kasa.

"Ina mai alfahari da ku, kokarinku ne yasa ake samun zaman lafiya a kasa, ina mai farin cikin cewa yanzu an samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka gabata," a cewar Buratai.

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwan ta yi 'tafiyar yaji' da mutane 30 a Abuja

Buratai ya bawa sojojin tabbacin cewa rundunar soji za ta dauki dawainiyar yi mu su magani koda kuwa kaiwa bukatar fitar da mutum zuwa kasashen ketare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng