Ibrahim Magu ya kara shiga matsala: DSS na neman takardar bayyana kadarorinsa daga CCB

Ibrahim Magu ya kara shiga matsala: DSS na neman takardar bayyana kadarorinsa daga CCB

- Kokarin tabbatar da zargin cin rashawa a kan Ibrahim Magu na kara kamari

- DSS sun hada kai da CCB don bankado wasu sabbin zargin rashawa a kan dakataccen shugaban EFCC

- An tattaro cewa jami'an tsaron farin kaya sun nemo takardar bayyana kadarori da Magu ya cike

A yayin da ake zargin Ibrahim Magu da rashawa, jami'an tsaron farin kaya sun sauya salo, inda suka koma bincike tare da CCB, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, DSS na neman samun takardar bayyana kadarori da dakataccen shugaban hukumar EFCC ya cike.

Idan za mu tuna, an damke dakataccen shugaban hukumar EFCC a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Duk da cewa DSS ta ce bata cikin wannan kamen amma ta gayyacesa ne don amsa tambayoyi.

Ibrahim Magu ya kara shiga matsala: DSS na neman takardar bayyana kadarorinsa daga CCB
Ibrahim Magu ya kara shiga matsala: DSS na neman takardar bayyana kadarorinsa daga CCB Hoto: The Cable
Asali: UGC

Magu, ya kwashe kwanaki 10 a tsare a kan zargin rashin biyayya da rashawa bayan korafin da Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a ya mika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga cikin manyan zargin da ake masa, kwamitin binciken na fadar shugaban kasar na bincikar Magu a kan siyan kadarori a Dubai tare da kalmashe kudaden da aka kwato a aljihunsa.

A ranar 22 ga watan Yuli, dakataccen shugaban EFCC ya fara kare kansa a kan zargin da ake masa ta bakin lauyansa, Wahab Shittu.

KU KARANTA KUMA: Na yi da na sanin goyon bayan Obaseki a 2016- Oshiomhole

A halin yanzu, DSS ta nemi yin binciken hadin guiwa don gano kadarorinsa a lokacin da ya zama shugaban hukumar.

"DSS ta tunkari CCB don duba takardar kadarorin da ya mallaka. Hukumar ta nemi yin binciken hadin gwiwa tare da kotun da'ar ma'aikatan. Tuni CCB ta fara ba hukumar hadin kai," wata majiya ta tabbatar.

A baya mun kawo cewa Femi Adesina, ya ce kwamitin bincike na fadar shugaban kasar ya tsare Magu ne don tabbatar da cewa ba a taba takardu masu muhimmanci ba.

Adesina ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan talabijin na Channels mai suna "siyasarmu a yau".

Hakazalika, lauyan Magu, Rosin Ojaomo, ya ce idan mai shari'a Salami ya gano cewa Magu bai aikata ko daya daga cikin zargin da ake ba, toh shugaban kasa ya mayar da shi kujerarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel