Zuwan Buhari Mali: PDP ta caccaki shugaban kasa Buhari

Zuwan Buhari Mali: PDP ta caccaki shugaban kasa Buhari

A ranar Lahadi ne jam'iyyar PDP ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattara ya je Mali kwantar da tarzomar siyasa, amma ya kasa shawo kan matsalar siyasa, tattalin arziki da tsaro da ke addabar Najeriya.

Jam'iyyar PDP ta ce tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa zai iya fita daga fadarsa har zuwa wata kasa, toh ya amsa kiraye-kirayen da ake masa a gida Najeriya, ThisDay.

PDP ta kara da cewa, tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya zuwa Mali, ya gaggauta ziyartar Katsina, Kaduna, Zamfara, Taraba, Binuwai, Borno, Adamawa, Sokoto, Yobe da sauran jihohin da kullum 'yan bindiga, 'yan ta'adda, masu kisa da masu garkuwa da mutane suka addaba.

A wata takardar da sakataren yada labarai na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar, ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da fifita halin da Mali ke ciki a kan tabarbarewar siyasa, rashin daidaituwar tattalin arziki, hauhawar rashawa, ci gaban ayyukan 'yan bindiga da zubar da jinin da ake yi a sassan kasar nan.

Ya yi watsi da alhakin da ke kansa inda ya gaggauta zuwa shawo kan na wasu.

PDP ta jajanta cewa 'yan kasar nan basu iya bacci saboda halayyar gwamnati amma ya tafi kasar ketare neman suna.

Zuwan Buhari Mali: PDP ta caccaki shugaban kasa Buhari
Zuwan Buhari Mali: PDP ta caccaki shugaban kasa Buhari. Hoto daga ThisDay
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda Gwamnan PDP ya sha 'ihu barawo' daga jama'arsa

Kakakin jam'iyyar ya kara da cewa: "A yayin da PDP bata da wata damuwa a kan zuwan shugaban kasar kwantar da tarzoma a Mali, amma kuma abin takaicin shine yadda Buhari ya yi tattaki har zuwa Mali yayin da ya ki duban kasarsa balle ya yi musu kara.

"Jam'iyyar mu ta amince da cewa shugaban kasan na samun bayanai a koyaushe a kan yadda tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan da tattalin arziki. Hakan yasa ya kamata ya dauka nauyin da ke kansa."

Kamar yadda yace, "shugaban kasar ya san kashe-kashen da ke aukuwa a Katsina, Kaduna, Zamfara, Taraba, Binuwai, Borno, Adamawa, Sokoto, Yobe da sauransu tare da kalubalen da dakarun sojin mu ke fuskanta a filin yaki. Amma ya bude kofarsa tare da ficewa zuwa Mali."

Ologbondiyan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma ya kasa yakar rashawa da ta zama babban tambarin mulkinsa. Sannannen abu ne idan aka ce jami'an sa na diba daga kudin kasa kamar yadda majalisa ke bankadowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel