Magu zai fara kare kansa ta hanyar sanar da jama'a kai tsaye - Lauya

Magu zai fara kare kansa ta hanyar sanar da jama'a kai tsaye - Lauya

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya ce a shirye ya ke ya fara amfani da kafafen sadarwa domin kare kansa daga dukkan tuhume - tuhumen da ake yi masa.

Magu ya bayyana hakan ne a cikin wani jaeabi da lauyansa, Wahab Shittu, ya fitar ranar Lahadi, inda ya ke musanta cewa an yi almundahana da kudaden da EFCC ta kwace daga hannun NNPC a lokacin Magu.

Shittu ya bayyana cewa kwamitin bincike da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa bashi da masaniya a kan wasu zarge - zargen badakala da ake alakantasu da Magu.

Lauyan ya bayyana cewa EFCC ta saka kudin da ta kwato a asusun NNPC bisa wani tsari da hukumomin biyu mallakar gwamnati da wasu manyan dillalan man fetur suka amince da shi, kuma an saka kudin ta asusun bai daya na kasa (TSA).

A cewar lauyan, duk wani mai shakku a kan hakan zai iya tabbatar da gaskiyar maganar ta hanyar tuntubar hukumar NNPC ko kuma ya ziyarci sashen adana bayanai na hukumar EFCC.

Shittu ya bayyana mamakinsa a kan yadda aka ko kadan maganar mayarwa da NNPC kudin bata kai gaban kwamitin binciken ba.

Sauran zarge - zargen da Shittu ya kare sun hada da batun zargin Magu da kin bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta bukata da kuma tsame wasu mutane daga tuhumar badakalar biliyan uku a hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS).

Magu zai fara kare kansa ta hanyar sanar da jama'a kai tsaye - Lauya
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Ya kara da cewa an kitsa zarge-zargen ne kawai da gan-gan domin a kunatatawa Magu sannan a bata sunansa.

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa ya yi nuni da cewa tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da lauyansa Wahab Shittu a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, sun so gabatat da wata takarda mai dauke da shafuka 34 gaban kwamitin.

DUBA WANNAN: Yakin neman zabe: An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo

Takardun na dauke da hujjojin kariya ga Ibrahim Magu, sai dai rahotanni sun bayyana cewa an hanasu gabatar da hujjojin gaban kwamitin fadar shugaban kasar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Magu da lauyansa sun bayyana gaban kwamitin binciken dake karkashin mai shari'a Ayo Salami da misalin karfe 1 na rana har zuwa karfe 6 na yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa ya isa fadar shugaban kasar tare da lauyansa Shittu da kuma wasu hadimansa.

Sai dai an ruwaito cewa Magu da Shittu ne kawai aka bari suka shiga cikin babban dakin gudanar da binciken, inda suka zauna na tsawon awanni.

Kundin hujjojin mai dauke da shafuka 34, ya kunshi hujjoji a rubuce, da hotuna, an kawo shi ne da nufin gamsar da kwamitin cewa duk tuhumar da ake yiwa Magu karya ce tsagoronta.

Jaridar Vanguard ta yi nuni da cewa lauyansa, Shittu, a wayar tarho ya ce ba a bari suka gabatar da wannan kundi a ranar Alhamis.

Kwamitin fadar shugaban kasar na tuhumar Magu akan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka saci kudin jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel