Labari da dumi: 'Yan sanda sun yi wa masarautar Shinkafi 'zobe'
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tsananta tsaro a farfajiyar fadar sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad Makwashi don tabbatar da tsaro ga lafiyar sarkin.
Wasu masu sarauta ke caccakar sarkin da mazauna Shinkafi a kan sarautar da ya bai wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Mohammed Shehu ya ce "masarautar ta gano cewa wasu na kokarin jagorantar zanga-zanga a cikin Shinkafi.
"Masarautar ta bukaci kariya daga rundunar 'yan sandan don gujewa tada tarzoma wanda muka amsa mata."
"Mun tura jami'anmu don sintiri a Shinkafi don tabbatar da zaman lafiya saboda kwamishinan 'yan sanda, CP Usman Nagogo ya ja kunnen jama'a a kan daukar doka a hannunsu.
"Idan mutum yana da matsala da wani, akwai hanyoyin mika korafi wadanda suka hada da kotu amma ba za mu amince wani ya tada mana tarzoma ba," Shehu ya yi bayani.
KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda 47 sun mika wuya ga jami'an tsaro hadin guiwa
Ya kara da jaddada cewa, abinda yake faruwa a Shinkafi ba wai tsare sarkin aka yi ba kamar yadda ake fadi ba, kariya ce aka bai wa sarkin.
Wani makusancin masarautar, Alhaji Murtala Dale ya ce "mun gano yunkurin wasu na kai wa sarki hari a yayin da yake kan hanyar zuwa sallar Juma'a. Hakan ne yasa muka bukaci kariya.
"Wannan duk yana zuwa ne saboda sarautar da aka bai wa Femi Fani-Kayode wanda wasu basu so."
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, wasu 'yan arewa basu jin dadin yadda tsohon ministan sufurin jiragen saman ke yin tsokaci marasa kyau game da arewa, 'yan arewa, Hausa/Fulani, Musulunci da kuma sarautar arewa ba.
Amma kuma, masarautar Shinkafi ta jihar Zamfara ta ce ba za ta iya janye sarautar da ta bai wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ba, saboda sarautar ba a iya kwaceta.
Sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad Maikwashe a makon da ya gabata, ya bai wa Fani-Kayode sarautar Sardaunan Shinkafi.
Amma wasu daga cikin 'yan masarautar da 'yan siyasa sun yi zanga-zanga a kan hukuncin Sarkin. Wasu masu sarauta biyar a masarautar Shinkafi sun tube rawaninsu a kan bada wannan sarautar ga Fani-Kayode.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng