Saudiya ta gindaya sabbin sharuda biyar ga masu aikin Hajjin bana
Yayin da ya rage sauran kwanaki basu wuce biyar ba a soma aikin hajjin bana a kasa mai tsarki, mahukuntan Saudiyya na ci gaba da aiwatar da muhimman shirye-shirye domin wannan babbar ibada.
A wannan karo dai mutane da aka bai wa damar gudanar da aikin hajjin a bana basu wuce 10,000 ba da kunshi mazaunan kasar kadai.
A bana babu wani bako daga ketare da gwamnatin Saudiyya ta ba izinin zuwa kasar domin gudanar da aikin hajji a sakamakon fafutikar da ake yi ta dakile bazuwar annobar korona a duniya.
Hukumomin Saudiya sun rage adadin mutanen da za ta ba izinin sauke farali a bana sakamakon yadda likafar annobar ke ci gaba babu sassauci.
A sanadiyar haka ne ya sanya Gwamnatin kasar ta sake sabunta sharuddan da maniyyatan bana za su kiyaye yayin wannna muhimmiyar ibada da ta kasance daya daga cikin rukunan Musulunci.
Kamar yadda sashen Hausa na kafar watsa labarai ta BBC ya ruwaito, jerin sabbin sharuda biyar da mahukuntan Saudiya suka shata sun hadar da;
Ya zama tilas duk maniyyatan bana su kasance ba sa dauke daya daga cikin cututtuka kamar; ciwon siga, larurar hawan jini, ciwon zuciya, cutar korona, da sauran larurorin da suka shafi numfashi.
Dole ne shekarun duk wani maniyyaci su kasance tsakanin 20 zuwa 65.
Ya zama wajibi duk wani maniyyaci ya kasance wannan shi ne aikin hajjinsa na farko, ma'ana bai taba yi ba a baya.
KARANTA KUMA: An ba hafsoshin tsaro N238bn don siyan makamai cikin shekaru biyu - Rahoto
Jigo cikin sharudan da aka gindaya wa maniyyatan bana shi ne dole ne su kiyaye dukkanin dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar cutar korona.
Daga cikin sharudan akwai dokar bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna, da kuma kasancewa sanye da takunkumin rufe fuska yayin shiga taron jama'a.
Haka kuma dole ne mahajjatan bana su killace kansu na tsawon kwanaki 14 gabani da kuma bayan an kammala aikin hajjin na bana domin a tabbatar da basu dauke da kwayoyin cutar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng