Yan sanda sun bazama bincike a kan lamarin matashin da ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwa a Kano

Yan sanda sun bazama bincike a kan lamarin matashin da ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwa a Kano

- Hukumar 'yan sandan jihar Kano sun bazama bincike a kan mutuwar dan shekara 22 da ya kashe kansa bayan masoyiyarsa ta bar shi

- Ashiru Danrimi ya halaka kansa a kwatas din Danrimi da ke karamar hukumar Kumbotso a ranar 23 ga watan Yuli

- Matashin ya soke kansa ne da wuka kamar yadda rundunar 'yan sandan ta sanar

Rundunar ‘yan sanda a Kano na bincike a kan mutuwar dan shekara 22 da aka rahoto cewar ya kashe kansa bayan masoyiyarsa ta yi watsi dashi saboda wani.

An tattaro cewa Ashiru Danrimi ya halaka kansa a kwatas din Danrimi da ke karamar hukumar Kumbotso a ranar 23 ga watan Yuli.

Yan sanda sun bazama bincike a kan lamarin matashin da ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwa a Kano
Yan sanda sun bazama bincike a kan lamarin matashin da ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwa a Kano Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

“Ya soke kansa da wuka saboda bai auri masoyiyarsa ba,” in ji hukumar ‘yan sandan.

Mahaifin Danrimi da ya halaka kan nasa ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda. Sai dai ba a ambaci sunan masoyiyar tasa ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya ce an tabbatar da mutuwar Darimi ne a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Zamfara ta raba raguna 5,000 da shanu 993

A wani labari na daban, mun ji cewa yaron wani Fasto da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyade, a yanzu haka an garkame su a dakin ajiye masu laifi na ofishin rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom da ke birnin Uyo.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, CSP N-Nudam Fredrick, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen mako.

Ya ce duk mutane shidan da ake zargi sun amsa laifin biyan bukatarsu ta sha'awa da budurwa matashiya mai kananan shekaru.

A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, ababen zargin sun shiga hannu ne bayan an shigar da korafi ga ofishin 'yan sandan kan ta'asar da suka aikata.

A cewar CSP Fredrick, kwamishinan 'yan sanda na jihar Edgar Imohimi, ya lashi takobin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato hakkin matan da aka ketawa haddi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: