Bayan umarnin PTF ya shude, Gwamnoni za su tattara keyar Almajiran da ke jihohinsu

Bayan umarnin PTF ya shude, Gwamnoni za su tattara keyar Almajiran da ke jihohinsu

- Har yanzu tsugune ba ta karewa Almajiran da ke Arewacin kasar nan ba

- Gwamnonin Yankin za su tattara masu bara su maida su duk inda su ka fito

- Wannan ya na zuwa ne bayan a da an dakatar da wannan aiki da aka fara

Jaridar The Punch ta ce gwamnoni 19 na yankin jihohin Arewacin Najeriya sun ce sun shirya cigaba da maida Almajirai zuwa garuruwansu na asali.

Rahoton ya bayyana jagoran kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, kuma sakatarenn gwamnatin jihar Filato, Danladi Atu ya yi wannan bayani a wata hira da aka yi da shi.

Atu ya ce: “Ba mu kammala dauke Almajirai a yankin ba. Gwamnonin Arewa za su zauna kwanan nan, su sa ranar da za a cigaba da maida Almajiran inda su ke fito.”

Danladi Atu ya ke cewa “Amma wannan zai kasance kusan zuwa bayan Sallah.”

KU KARANTA: Ana so Dogara su yi takarar Shugaban kasa da Tinubu a 2023 – kungiya

Bayan umarnin PTF, Gwamnoni za su tattara keyar Almajiran da ke jiharsu
Wasu Almajirai a Najeriya
Asali: Twitter

A cewar jagoran na NGF, akalla Almajirai 11, 000 aka maida gidajen da aka haife su a jihohin Arewa a lokacin da annobar COVID-19 ta soma aukuwa.

Idan ba za ku manta ba, annobar COVID-19 ta fara kamari ne a Najeriya a watan Mayu. Fiye da watanni biyu kenan ana fama da Coronavirus a kasar nan.

Mista Danladi Atu ya ce a baya gwamnonin yankin sun rika maida almjarai, amma yanzu an dakatar da wannan lamari ne domin bin umarnin shugaban kasa.

Kwanakin baya sakataren gwamnatn tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya haramtawa gwamnonin Arewa yawo da almajrai daga wuri zuwa wuri.

Yanzu da kwamitin PTF ya dakatar wannan doka, za a koma aikin da aka faro na maida Almajran zuwa kauyuka da garuruwan da iyayensu su ke inji Atuku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel