Sunayen filayen jiragen sama 14 da ke hada-hada a Najeriya

Sunayen filayen jiragen sama 14 da ke hada-hada a Najeriya

A ranar Juma’a, 24 ga watan Yulin 2020, filayen tashi da saukar jiragen sama 14 gwamnatin tarayya ta amince da su koma aiki.

Sannan a ranar 8 ga watan Yulin 2020 ne gwamnatin tarayyar ta bude filayen sauka da tashin jiragen sama na Legas da Abuja.

Har ila yau a ranar 11 ga watan Yuli aka bude filayen jiragen sama hudu da suka hada da na Fatakwal da ke jihar Ribas, filin sauka da tashin jiragen sama na mallam Aminu Kano, Maiduguri da kuma Owerri.

Kungiya daga hukuma kula da kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu, sun dudduba filayen sauka da tashin jiragen saman kafin budesu.

Sunayen filayen jiragen sama 14 da ke hada-hada a Najeriya
Sunayen filayen jiragen sama 14 da ke hada-hada a Najeriya Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Daya daga cikin abubuwan da suka duba kafin amincewa da bude filayen sauka da tashin jiragen saman shine tabbatar da dokokin dakile yaduwar muguwar annobar korona tare da tabbatar da tsafta.

Darakta Janar na NCCA, Kyaftin Musa Nuhu ya ce akwai yuwuwar kungiyar NCAA din ta kwashe mako daya tana duba sauran filayen sauka da tashin jiragen saman kafin a budesu.

Amma kuma, a yau Lahadi, filayen sauka da tashin jiragen sama 14 NCAA ta amince da budesu.

KU KARANTA KUMA: Masarautar Katsina ta soke shagulgulan babbar sallah

Ga jerin filayen jiragen saman 14:

1. Filin tashi da saukar jirage na Victor Attah da ke Uyo; Akwa Ibom

2. Filin tashi da saukar jirage na Kaduna, da ke Kaduna

3. Filin tashi da saukar jirage na Yola da ke Adamawa

4. Filin tashi da saukar jiragen sama na Margaret Ekpo da ke Calabar, Cross River

5. Filin tashi da saukar jiragen sama na Sultan Abubakar da ke Sokoto

6. Filin tashi da saukar jiragen sama na Birnin Kebbi da ke Kebbi

7. Filin tashi da saukar jiragen sama na Yakubu Gowon da ke Jos, jihar Plateau

8. Filin sauka da tashin jiragen sama na Benin da ke Benin jihar Edo

9. Filin sauka da tashin jiragen sama na Maiduguri

10. Filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano

11. Filin sauka da tashin jiragen sama na Yola

12. Filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed, Lagos

13. Filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja

14. Sai filin sauka da tashin jiragen sama na Port Harcourt , Omagwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel