Ambaliyar ruwan sama ta tafi da mutane 30 a Abuja

Ambaliyar ruwan sama ta tafi da mutane 30 a Abuja

A kalla mutane 30 ake fargabar cewa ambaliyar ruwa mai karfi ta yi awon gaba dasu a yankin Gwagwalada da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Kazalika, wasu da dama sun rasa gidajensu sakamakon mamakon ruwan saman da aka maka da misalin karfe 3:00 na ranar Asabar.

Ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da gine - gine da gidaje masu yawa tare da sauyawa motoci da yawa muhalli.

Motsin motoci da sauran ababen hawa ya tsaya cak a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja sakamakon shafe titi da ruwan saman ya yi.

Ruwa ya shanye babbar gadar kogin Gwagwalada wacce ke kusa da tashar motoci ta 'Wazobia'.

Mazauna yankin Gwagwalada sun bayyana cewa sun dade basu ga irin wannan mamakon ruwan sama ba.

Ruwan da ya kwanta a harabar wani bankin zamani da ke bakin babbar hanyar ya hana jama'a amfani da na'urar fitar da kudi ta bakin.

Ambaliyar ruwan sama ta tafi da mutane 30 a Abuja
Ambaliyar ruwan sama
Asali: Depositphotos

Jaridar The Nation ta rawaito cewa ruwan saman ya yi awon gaba da duk wasu gidaje da ke gefen guraben taruwar ruwa, lamarin da ya tilasta jama'a yin kaura domin neman mafaka.

An ga kayayyakin amfani irinsu; tebura, katifu, kwanukan girki, da sauransu suna iyo yayin da ambaliyar ruwan ta kwasosu daga gidjen jama'a.

DUBA WANNAN: FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19

Haka jama'a suka tsaya cikin takaici suna kallon yadda ambaliyar ke yin tafiyar yaji da dukiyoyinsu.

Har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, babu wata hukumar gwamnati da ta fitar da kididdigar asarar da ambaliyar ta haifar.

Sai dai, wani jami'in hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) ya tabbatar da cewa labarin annobar ya isa zuwa kunnen manya.

Majiyar ta bayyana cewa ta aika mota da wasu jami'ai domin bayar da agajin gaggawa a yankin da ambaliyar ta fi karfi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel