FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19

FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19

Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya shaida cewa kowacce jiha daga cikin jihohi 36 na Nigeria da kuma babban birnin tarayya Abuja (FCT), za ta samu naira miliyan 100, domin ci gaba da yakar cutar COVID-19.

Mr Ehanire ya bayyana hakan a taron mako mako na kwamitin yaki da cutar na fadar shygaban kasa (PTF) a ranar Alhamis, a fadar shugaban kasa.

"Ina mai sanar da ku cewa kowacce jiha tare da babban birnin tarayya Abuja zata samu tallafin yaki da cutar COVID-29 ta hannun shirin bunkasa yaki da cututtuka (REDISSE).

"Da wannan tallafin, kowacce jiha da ke a Nigeria zata samu tallafin naira miliyan 100 domin dakile yaduwar cutr. Da zaran an kaddamar da tallafin asusun BHCPF zai fara aiki," a cewarsa.

Bankin Duniya ne ya samar da shirin REDISSE domin tallafawa duk kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS, a lokacin da aka fara yakar cutar Ebola tsakanin 2014 zuwa 2015.

Shirin na taimakawa kasashen wajen basu damar yin hadaka, domin cike gurbin matsalolin yaduwar cututtuka da kuma barkewarsu a kasashen Afrika ta yamma.

KARANTA WANNAN: Yadda aka binne gawar Tolulope Arotile - Matukiyar jirgin yakin NAF

FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19
FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19
Asali: UGC

A wani labarin, tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da lauyansa Wahab Shittu a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli sun so gabatat da wata takarda mai dauke da shafuka 34 gaban kwamitin.

Takardun na dauke da hujjojin kariya ga Ibrahim Magu, sai dai rahotanni sun bayyana cewa an hanasu gabatar da hujjojin gaban kwamitin fadar shugaban kasar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Magu da lauyansa sun bayyana gaban kwamitin binciken dake karkashin mai shari'a Ayo Salami da misalin karfe 1 na rana har zuwa karfe 6 na yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa ya isa fadar shugaban kasar tare da lauyansa Shittu da kuma wasu hadimansa.

Sai dai an ruwaito cewa Magu da Shittu ne kawai aka bari suka shiga cikin babban dakin gudanar da binciken, inda suka zauna na tsawon awanni.

Kundin hujjojin mai dauke da shafuka 34, ya kunshi hujjoji a rubuce, da hotuna, an kawo shi ne da nufin gamsar da kwamitin cewa duk tuhumar da ake yiwa Magu karya ce tsagoronta.

Jaridar Vanguard ta yi nuni da cewa lauyansa, Shittu, a wayar tarho ya ce ba a bari suka gabatar da wannan kundi ba a yau (Alhamis).

"Amma dai zamu koma gobe (Juma'a)," a cewar lauyan, duk da cewa bai bayyana dalilin da ya sa aka hanasu gabatar da hujjojin ba.

Kwamitin fadar shugaban kasar na tuhumar Magu akan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka saci kudin jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel