Babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban Nigeria a 2023 - Kungiyar Arewa

Babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban Nigeria a 2023 - Kungiyar Arewa

- Kungiyar Arewa mai rajin wanzar da zaman lafiya da tsaro (AYPS) ta goyi bayan wani rahoto na cewar Bola Tunubu zai tsaya takarar shugaban kasa

- Kungiyar ta kalubalanci ministan ayyuka da daukar ma'aikata, Chris Ngige, na kakkausan furucin da yayi kan jagaban APC

- Kungiyar AYPS ta ce alamta Tinubu a matsayin abokinsa da Ngige yayi gaban kwamitin majalisar tarayya cin fuska ne

Rahoton kudirin Bola Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya samu karbuwa a wajen wata kungiyar arewa mai rajin wanzar da zaman lafiya da tsaro (AYPS).

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, ta ce babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban kasa idan har haka Allah ya nufa.

Jaridar Tribune ce ta wallafa wannan rahoto, inda ta ruwaito kungiyar AYPS na cewa ma damar Allah ya amince, to babu wanda ya isa ya hana Tinubu cin zaben 2023.

AYPS ta fitar da sanarwar ne a martanin da ta mayarwa ministan ayyuka da daukar ma'aikata, Chris Ngige, akan jagaban jam'iyyar ta APC.

Kungiyar ta Arewa ta zargi Ngige da furta kalaman rashin da'a akan Tinubu gaban kwamitin majalisar wakilan tarayya.

KARANTA WANNAN: Mata sun yi zanga - zanga tsirara a Kaduna

Ta ce ministan ya kira Tinubu da abokinsa a lokacin da yake musayar baki da wani mamba na kwamitin, James Faleke, hakan kuma rashin da'a ne.

Babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban Nigeria a 2023 - Kungiyar Arewa
Babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban Nigeria a 2023 - Kungiyar Arewa
Asali: Twitter

Kungiyar ta yi ikirarin cewa kalaman Ngige na nuni da cewa wasu mutane dake cikin wannan gwamnatin na adawa da kudurin Tinubu na zama shugaban kasar Nigeria.

AYPS ta bukaci Ngige da ya roki afuwar Tinubu akan kalamansa da kuma shawartar duk wadanda ke adawa da kudirin jagaban APC dasu kauracewa furta kalaman batanci akansa.

A wani labarin kuma, tuni dai shirye shirye kan wanda zai zama shugaban kasar Nigeria na gaba ya dauki mikati inda wasu 'yan Nigeria ke ganin cewa Kudu ne ya kamata su karbi mulki.

A wani rahoton jaridar Vanguard, 'yan Nigeria da ke da irin wannan ra'ayi sun hada da wani jigon APC a Kano, Brig-Janar Idris Dambazzau; mai fada aji Alhaji Tanko Yakassai; Chief Edwin Clark, da shugaban al'ummar Afenifere, Chief Ayo Adebanjo.

Sauran masu irin wannan ra'ayin sun hada da tsohon dan majalisa, Junaid Mohammed; tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa Chief Bode George; Chief Ebenezer Babatope.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel